‘A cece jama’a’ – Sakon Aisha ga Buhari

0

Uwargidan shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira da a samar wa mutane da tsaro a fadin kasar nan.

Aisha ta rubuta haka ne a wata sabuwar waka mawaki Adam Zango ya saki ranar Juma’a inda ya ke koka wa da yadda ake fama da rashin tsaro a fadin kasar nan, musamman a yankin Arewa.

Aisha ta saka hotunan hafsoshin tsaron Najeriya da na Mijinta a wuraren da mawaki Zango ke jero matsalolin rashin tsaro da ake fama dashi.

Idan ba a manta ba, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta dade ta sukar gwamnatin mijin ta.

Ta dade tana yin korafin rashina korafin yadda mijin ta, shugaba Buhari ke mulkin ƴan Najeriya.

Saidai kuma wasu na ganin a wannan lokaci da mijinta da makarraban gwamnatin sa ke shan zafin ƴan zanga-zangar #EndSARS a fadin kasar nan, sun ce basu ga dacewarta ta rika kara ruruta wutan dagula ayyukan gwamnati ba.

Share.

game da Author