An dage dakatarwar da Najeriya ta yi wa wasannin kwallon kafa da sauran wasanni daban-daban, watanni bakwai bayan da annobar korona ta tilasta dakatar da wasannin.
A ranar Alhamis ce Kwamitin Shugaban Kasa Kan Cutar Korona tare da hadin guiwa da Ma’aikatar Wasanni ta Kasa, su ka janye dakatarwar.
Ministan Wasannin Sunday Dare, ya ce dage dakatarwar wasu alamu ce da ake maraba da su wajen dawo da martabar wasannni a kasar nan.
Sai dai ya ce NCDC wasannin kadai ta ce a ci gaba, amma banda taron cincirindon jama’a ‘yan kallo.
Kafin a dage dakatarwar, jama’a da dama sun rika nuna damuwar su ganin yadda aka bada iznin ci gaba da sauran harkoki, amma banda wasanni.
Tuni dai aka bada umarnin bude wuraren dandazo da cincirindon mutane, kamar kasuwanni, masallatai da coci-coci.
Kenan wannan umarni na ci gaba da buga wasannin kwallo, ya na nufin za a dawo da buga gasar Kwararru ta League, a sitadiyan, ba tare da ‘yan kallo ba.