Masu zanga-zangar #EndSARS sun yi wa gwamnan Osun Gboyega,ruwan duwatsu, an kassara mutum biyu

0

A cigaba zanga-zangar #EndSARS da matasan Najeriya keyi, a jihar Osun, gwamnan jihar Gboyega ya sha da kyar a hannun masu zanga-zanga.

Gwamna Gboyega ya biyu ta titunan da matasa suka daddatse zai wuce, amma kafin ya ankara sun fara yi masa luguden duwatsu babu kakkautawa.

Haka ya samu ya kauce da gudun tsiya. Saidai sun farfasa masa wasu motocun dake tawagar sa.

Matasa na ci gaba da zanga-zangar #EndSARS a fadin kasar nan. A jihar Legas da Abuja inda abin ya fi tsanani abin yana neman yafi karfin gwamnatun jihohin.

Matasa sun tirje sai Buhari yayi musu jawabi sannan kuma an bi musu duk bukatun su.

Gwamnati ta ci gaba da tausa masu zanga-zangar inda a ranar Juma’a mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kansa ya aika wa ƴan Najeriya sakon musamman cewa su yi haku su ba gwamnati dama ta ci gaba da ayyykan sauye sauyen ci gaba da ta sa a gaba musamman game da yi wa rundunar ƴan sanda garambawul.

Share.

game da Author