Na yi da-na-sanin shugabantar kwamitin binciken Magu – Maisharia Salami

0

Maisharia Ayo Salami ya yi dana sanin shugabantar kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa don bincikar tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da yayi.

Wannan kalamai da Salami yayi sun fito ne daga wasu Lauyoyi biyu dake wurin a lokacin da Maisharia Salami ya bayyana haka.

Lauyoyin masu suna Tosin Ojaoma da Zainab Abiola, duk sun shaida wa PREMIUM TIMES a lokutta daban daban cewa maisharia Salami ya bayyana da bakin sa cewa yayi dana sanin saka kansa a cikin wannan bincike.

” Muna zaune a lokacin da Salami ya zo ya zauna sai ya girgida kai ya ce, na yi nadamar shugabantar wannan kwamiti na binciken Magu.

” Salami ya cire kyallen goge fuska yana ta goge fuskar sa yana cewa, kaico na yi danasanin saka kaina a cikin wannan kwamiti din. Ya rika goge fuskarsa.

” Na tambayeshi cewa me ya sa ya ke cewa haka? Amma bai amsani ba, yana ta maimaita cewa gaskiya yayi da-na-sanin wannan aiki da yake yi.

Lauyan ya ce ko da suka tambayeshi ko don ya ga cewa har yanzu ba a iya samun Magu da aikata laifi ko daya ba. Salami ya cigaba da goge fuskarsa ne kawai yana cewa yayi nadamar shiga cikin wannan kwamiti.

Kwamitin Salami, ya nemi a kara masa lokaci domin ya karkare aiki kafin ya mika wa gwamnati rahotan sa.

Share.

game da Author