Idan muka ragargaza siyasar Ubangida a Edo, zamu garzaya Legas mu fatattaki Tinubu – Inji Obaseki na PDP

0

Ɗan takarar gwamnan jihar Edo a zaɓen Asabar, na jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki ya shaida cewa zai baiwa jam’iyyar APC kunya a zabe gwamnan jihar dake tafe.

Obaseki ya ce bayan nasara da zai yi zai kawo karshe siyasar ubangida a jihar.

” Idan jam’iyya ta PDP ta gama da Edo, ta kuma gama da siyasar ubangida, za kuma mu ɗungu mu dira jihar Legas. Zamu je can ita ma mu gama da siyasar Ubangida mu ragargaza Tinubu.

” Jigon Ubangida a siyasar Najeriya, ‘Bola Tinubu’, ya fito ya yi suka akan mu ƴan PDP, abinda ya ke tada masa hankali shine ganin yadda zamu kawo karshen siyasar ubangida a Edo ranar Asabar, sannan kuma mu dunguma zuwa Legas domin fatattakar shi da karya siyasar ubangida a jihar.

Waɗannan kalamai na martani sun biyo bayan tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ya caccaki gwamna Obaseki a wata hira da yayi da Talbijin ɗin TVC ranar Laraba.

Obaseki ya yi wannan kuri ne a wajen taron gangami na jam’iyyar PDP da aka yi a Edo.

Sannan ya kara da cewa nasara na tare da su a wannan zabe da tafe.

” Akwai akalla ƙungiyoyi sama da 100 da yanzu haka sun yi mana alkawarin PDP za su zaɓa, saboda haka bamu shakkan wannan zaɓe.

Abinda Tinubu Yace

Jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ya yi kira ga ƴan kuma har Edo su zaɓi ɗan takarar APC a zaɓen ranar Asabar.

” Gwamnan dake kai mulki a jihar, ya rusa turaku da aka kakkafa don cigaban jihar wand gwamnatocin baya suka yi. Ya tarwatsa majalisar jihar sannan ya kasa tabuka abin azo a gani a jihar.

Tinubu ya ƙara da cewa lokaci yayi a taka masa birki a wancakalar da su a zaɓen.

Share.

game da Author