Gwamna Zulum ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan jami’an gwamnati da Boko Haram suka kashe a harin kwantar bauna

0

Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum, ya tabbatar da kisan jami’an tsaron da 11 da Boko Haram su ka yi a ranar Juma’a.

Zulum ya yi wannan bayani a ranar Asabar, lokacin da ya ke nuna jaje da takaicin rashin wadannan zaratan jami’an tsaro su 11.

A ranar Juma’a PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Boko Haram sun kai wa jami’an INEC tsaron Zulum harin kwanton-bauna, su ka kashe 15 a hanyar su ta zuwa garin Baga daga Maiduguri.

Cikin wata takarda da Kakakin Yada Labarai na Gwamna, Isa Gusau ya fitar a madadin Zulum a ranar Asabar, gwamnan ya ce kisan jami’an tsaron ya yi masa ciwo matuka.

Da ya ke karin bayani, ya ce Gwamna ya shirya zuwa taron maida al’ummar garin Baga gida, bayan tsawon lokacin da su ka shafe ba su garin, sanadiyyar hare-haren Boko Haram.

“To sai aka raba tawagar gida uku: Akwai tawagar jami’an gwamnati, akwai tawagar ‘yan rakiyar Gwamna tare da Gwamna din. Sai kuma tawagar jami’an tsaro.

“To shi gwamna da tawagar sa ba a motoci su ka tafi Baga daga Maiduguri ba. A jirgin sojoji aka dauke su, wato helikwafta.

“Tawagar jami’an tsaro masu rufa baya, ‘yan ko-ta-kwana, su ne Boko Haram su ka ritsa su ka yi masu kwanton-bauna.

“Lokacin da aka masu hari, shi tuni Gwamna har ma ya sauka misalin 11 na safe, kuma ya na jawabi a wurin taro.”

Gusau ya ce Zulum ba ya cikin ayarin da Boko Haram su ka kai wa hari.

Idan ba a manta ba an kai wa Zulum hari a kusa da Baga, cikin watan Agusta, wanda ya zargi sojoji da hannu a ciki.

Yayin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ikirarin sun karya lagon ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, a lokacin kuma su ke kara kaimin kashe sojojin Najeriya.

Share.

game da Author