SABON SARKIN ZAZZAU: Na gama littafi na biyu yanzu na shiga na uku – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yanzu ya fada cikin littafi na uku na karance-karancen yadda zai nada sabon sarkin Zazzau da wanda zai nada.

El-Rufai ya rubuta a shafinsa ta tiwita cewa, ya cikin karatun littafin sa na karshe kuma na uku, kafinnan ya waiwayi rahoton ma’aikatan Harkokin Maarautu na jihar bayan tantance sunayen da aka mika a gaban ta na mutum 11.

” Ina rokonku ku tayi da addu’a Allah ya yayi min jagora in zaba wa mutane sarki wanda zai dau saiti da cigaban zamani na wannan karni ta 2021 domin cigaban al’umma da masarautar Zazzau.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi mutane su daina yada labaran Karya, cewa wai an mika wa gwamnatin jihar sunayen mutum 11 dake son a nada su sarautar sarkin Zazzau.

El-Rufai ya rubuta a shafinsa ta tiwita cewa, mutum 11 ne suka rubuta neman a nada su sarkin Zazzau, kuma dukka wadannan sunaye na gaban kwamishinan harkokin masarautu na jihar Kaduna. El-Rufai ya ce idan suka gama aiki akai za su turo masa ofishin sa daga nan kuma sai ya bayyana wanda ya yi nasarar zama sarkin.

SARAUTAR ZAZZAU: Ina karatun littafi na biyu

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya saka a shafinsa ta tiwita cewa yanzu ya na karatun littafi na biyu dake bayanin yadda aka nada Sarki Jaafaru Dan Isyaku mahaifin Yerima Mannir Jaafaru da marigayi sarki mai rasuwa Shehu Idris.

Yace da zaran kwamishinan harkokin masarautu na jihar ya kammala aiki akan wadanda aka aiko da sunayen su, daidai ya kammala karatun sa, sai ya bayyana sabon sarki.

Idan ba a manta ba, Iyan Zazzau, Bashar Aminu, ne ya samu mafiyawan maki cikin sunayen da aka mika wa gwamnan jihar Kaduna domin zaben daya daga cikin su ya zama sarkin Zazzau din.

Wanda da yawa ake ganin zai iya zama sarki kuma makusancin gwamnan Kaduna, Ahmed Bamalli bai ma samu dacewa an zabe shi cikin jerin wadanda aka mika wa gwamnan ba.

Iya Bashar Aminu daga gidan Katsinawa, ne ya samu maki da ya fi yawa, ya samu maki 89%, sai Yeriman Zazzau da ya samu maki 87%, sai Turakin Zazzau Aminu Ideis dake da maki 53%.

Cikin masu zaben sabon sarki, uku sun zabi Iya Bashar, shi kuma Yerima da Turaki sun samu ƙuri’a daidai.

Idan har Iya ya samu kujerar sarautar Zazzau, gidan Katsinawa za su ci gaba da sarautar ke nan fiye da shekara 61 a kasar Zazzau.

Wani abinda da ya daure wa mutane kai shine wancakalar da sunan Magajin Garin Zazzau da masu zaben sabon sarki suka yi.

Duk da cewa ana ganin kusancin sa da gwamna, sai gashi tun daga gida basu yarda masa ba.

Sai dai ba anan gizo ke sakar ba, domin koma waye aka tsayar, sai wanda gwamna ya ga yafi dacewa da salon mulki na zamani da kuma wanda ya kwanta masa, domin shine wuka shine nama.

Tuni dai an ce gwamna El-Rufai ya kira kwamitin tsaro na jihar tun da safiyar Juma’a domin su kinkintsa da shirin ko ta kwana.

Share.

game da Author