An yi wa mata masu ciwon yoyon fitsari 31 fida a jihar Bauchi

0

Babban asibitin Gamawa dake karamar hukumar Gamawa jihar Bauchi ta ti wa mata 31 dake fama da yoyon fitsari fida.

Shugaban gidauniyar kula da Mata masu yoyon fitsari (FFN) Musa Isa ya bayyana haka a taron wayar da Kan mutane game da ciwon yoyon fitsari na tsawon kwanakin biyar da aka yi a asibitin.

Asibitin Gamawa tayi fidan ne tare da hadin gwiwar gwamnati kasar Canada a karkashin shirinta na yaki da wasu al’adun gargajiya masu hadari ga lafiyar mutane, hukumar UNFPA, ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bauchi da gidauniyar kula da masu fama da ciwon yoyon fitsari FFN.

Isa ya ce mata 31 din da aka yi wa fidan na daga cikin mata 53 dake fama da wanna lalura a jihar.

“Daga cikin matan da aka yi was fidan akwai ‘yan Mata masu shekaru 6,11,14 da 16 da suka kamu da wannan lalura a dalilin fyade da kaciya.

Ya ce asibitin ta dauki likitoci biyu da ma’aikatan jinya guda hudu domin kula da masu fama da matsalar ciwon yoyon fitsari.

Isa ya yi kira ga mata dake fama da wannan matsala da su gaggauta zuwa asibiti domin samun magani.

Yoyon fitsari matsala ce dakan kama mace a dalilin yin dogon nakuda a haihuwa, yi wa mace kaciya da fyade.

Yin fida, da cin abincin dake inganta garkuwar jikin na daga cikin hanyoyin warkewa daga cutar.

Idan ba a manta ba wani sakamakon Bincike da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya, UNFPA ta yi a Najeriya da ta gabatar a Mayu ya nuna cewa a duk shekara mata 12,000 ne ke kamuwa da matsalar yoyon fitsari a kasar.

Wakiliyar UNFPA, Ulla Muller ta ce mata 148,000 ne ke fama da wannan matsala a Najeriya kuma a duk shekara sai an samu mata akalla 12,000 da suka kamu da ciwon, cewar Muller.

Ta ce UNFPA ta dade tana tsara matakai don kare mata a Najeriya daga kamuwa daga cutar.

Wadannan matakai sun hada da ilmantar da mata game da dabarun bada tazarar haihuwa, wayar da kan mutane game da ciwon da horas da ma’aikatan kiwon lafiya hanyoyin kula da masu fama da ciwon.

Share.

game da Author