Kungiyar likitocin hakora ta kasar (NDA) ta yi kira ga mutane da su guji amfani da da man da ake wanke hakora da shi don ya saka hakora suyi farare kal-kal ba tare da samun shawarar likita.
Kungiyar NDA ta ce amfani da man kan sa a faduwar hakora sannan suna lalacewa.
Likitocin sun ce rashin tsaftace baki na cutar da hakoran mutum sannan rashin amfanin da man wanke baki da ya kamata, yawan cin zaki, Shan bakin shayi wato coffee, daukan ciki, kamuwa da cutar siga, Shan taba da sauran su na daga cikin abvubuwan dake canja kalan hakoran mutum.
NDA ta shawarci mutane da su rika garzaya asibitin hakori domin a duba lafiyar hakoran su da basu shawara kan yadda za su tsaftace hakora.
Idan ba a manta ba a watan Janairu ne sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa kashi 15 zuwa 58 na mutane a Najeriya na yawan kamuwa da cututtukan dake kama hakora.
Binciken ya kuma kara nuna cewa kashi 30 bisa 100 daga cikin su kan dade suna fama da wadannan cututtuka ba tare da sun je asibiti ba.
Hakan na da nasaba ne da rashin wanke hakora yadda ya kamata da mutane ke yi.
Bayan haka sakamakon binciken da ‘National Smile Mouth’ ta gudanar ya nuna cewa mutane Biyu cikin mutane Uku a Najeriya basu da masaniya game da yadda ya kamata wanke baki da hakora.
A dalilin haka wani likita a shafinsa na tiwita yayi kira ga mutane da su daina kuskure baki da ruwa kaf bayan an goge hakora da man goge hakorar cewa dan barin kumfar na kara inganta tsaftar baki da karfin hakorar.