A tsawon rayuwa na ba na zaton an taba shiga irin wannan matsi na kunci a Najeriya – Inji Farouk Adamu

0

Jigo a Jam’iyyar APC kuma makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan tsohon dan majalisar tarayya, Farouk Adamu Aliyu, ya tabbatar da cewa mutanen Najeriya  sun fada cikin matsanancin hali a kasar nan a wannan lokaci na mulkin Buhari.

Da ya ke tattaunawa da BBC Hausa, Farouk Aliyu ya ce” Ni ma na shekara 60 a duniya yanzu amma ban taba ganin an shiga matsi irin haka ba.

Sai dai kuma Ɗan siyasan ya ce an samu cigaba da dama a kasa Najeriya duk da matsin da aka shiga

” A da kafin wannan gwamnati, idan zaka Kano zaka gamu da shingen ƴan sanda masu yawan gaske, saboda rashin tsaro, haka kuma masu acaba suma a duk lokacin da suka iso wannan wuri sai sun sauka daga baburan su.

Adamu ya kara da cewa sun gaya wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa ya kamata a yi wa shugabannin rundunonin tsaro garambawul, wato a canja manyan hafsoshin su.

” Toh da yake shi tsohon soja ne kuma shine shugaban kasa, shine yake da cikakken iko akan komai, kuma ya fi mu sani bai yi haka ba. Ba a canja kwamandoji a lokacin yaki. Shi ya fi mu sani, amma kuma an bashi wadannan shawarwari.

” Da ya ke tsarin Dimokradiyya ake yi, wani abin ko da ba daidai bane da yake tsari ne na jama’a, inda suka fi karkarata a kai nan ya kamata a bi saboda koda daga baya ba a daxe ba za ka iya fitiwa kace su jama’an suka ce ayi haka.

Da yake tsokaci akan taadar abinci da ake fama da shi a kasar nan, Farouk Adamu ya ce tabbas akwai tsadar abinci da ake fama dashi a kasar, amma kuma gwamnati ta tabuka abin a yaba a wannan fannin.

” Da badun mun noma abincin mu ba da bullowar annobar Korona da kowa ya shiga tasko, domin za a samu karancin abinci da tsadar sa fiye da yadda yake a yanzu. Da kudin ka ma baza ka samu abincin ba.

Ya ce duk da cewa wasu manoma da aka rabawa kudin bashi na tallafin noma sun ki dawowa da su.

” Wasu fa da aka basu bashin kudin, hamdala kawai suka yi suka caske kudaden a aljihunsu suka kama gabansu kawai. Wai rabonsu ne ya iske su daga sama gasassa.

Akarshe yayi kira ga ƴan kasuwa su ji tsoron Allah su rika jinkan mutane, su daina tsawwala wa kayan su kudi.

Share.

game da Author