Jihohin Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Oyo, Osun, Ekiti da wasu jihohi shida sun kasa biyan ayyukan gudanar da tafi da gwamnati da kudaden shigar da su ke samu a cikin 2019.
Rahoton da Kungiyar Sa-ido Kan Yadda Ake Kashe Kudaden Gwamnati, wato BudgiT ta fitar, ya nuna cewa wadannan jihohi 13 sun kuma kasa rika zuba kason biyan bashin da ya kamata su rika zubawa duk wata, domin rage nauyin tulin bashin da ake bin su.
Sauran jihohin biyar sun hada da Benuwai, Filato, Kogi, Cross River da Abia.
BudgiT ta ce jihohin da wannan abu ya fi shafa sun hada da Oyo, Kogi, Osun da Ekiti, Jihar da Gwamnan ta ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Dalla-dallar wannan bayani dai na kunshe nea cikin rahoton na BudgiT, wanda ta ce rahoton zai taimaka wa masu tsare-tsaren harkokin bunkasa ci gaban kasa da tattalin arziki su fahimci inda inda ake samun tawaya sosai.
“Ko tantama babu bashin da ya yi wa jihohi katutu da kuma rashin iya tsara tafarkin inganta tattalin arziki tare da bata shekaru 10 a banza su na aikin-baban-giwa da kashe makudan kudade inda ba su kamata ba, sun taimaka wajen shimfida wa jihohi karkatacciya hanyar narkar da kudade a wuraren da ba su da muhimmanci a ci gaban jihohin.” Inji rahoton BudgiT na ranar Alhamis.
BudgiT sun ce wannan rahoto dai a takaice ya na nufin wadannan jihohi ba su iya ciyar da kan su ko da tsawon wata daya a shekara, tilas sai sun jira kudade daga Gwamnatin Tarayya a duk karshen wata.
“Jihohin da ke da karfin daukar nauyin kan su sun hada da Ribas ta farko, sai Anambra, Ogun, Lagos.
“A jerin ‘yan Allah-ba,-ku-mu-samu kuwa, Bayelsa ce ce farko Osun, Ekiti da Filato.
“Sauran jihohi 23 masu iya tabuka daukar nauyin biyan kudaden bukatun gwamnati na yau-da-kulkum da rage basussuka, 8 daga cikin sai da ‘yan dabaru su ke iyawa kuma su dan rika rage basussukan.