Yadda zan zabi Sabon Sarkin Zazzau – El-Rufai

0

A daidai ana ta zuba ido aga ko wanene gwamnatin Kaduna zata nada sabon sarkin Zazzau, gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bayyana yadda zai zabi sabon sarkin.

El-Rufai ya saka a shafin sa ta Facebook yana karanta wata jibgegiyar littafi kan yadda turawan mulkin mallaka suka rika nada sarakunan kasar Zazzau tun daga 1800 zuwa 1950 wanda Prof MG Smith ya rubuta.

Yanzu dai komai ya karkata zuwa Zariya domin can ne ake ta daka lissafe lissafen ko wa ye zai zama sabon sarkin Zazzau.

Zuwa yanzu dai akwai alamar cewa Yeriman Zazzau Mannir Jaafaru wanda makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne na daga cikin wadanda ake ganin tabbas akwai yiwuwar ya zama sabon sarkin Zazzau.

Mannir Jaafaru ɗan tsohon sarki Jaafaru Ɗan Isyaku ne wanda bayan ya rasu Sarki Aminu ya ɗare kujerar sarautar Zazzau ɗin, wato dai bai gaji mahaifin sa ba.

A tsawon rayuwar sa Mannir ya fito ya nuna karara sarautar ce kawai a gaban sa, ya riƙa yi mata hidima ya na kai kansa ga ita sarautar ba da wasa ba.

Wasu na ganin kusantar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sa ya cimma burin sa na zama sarkin Zazzau. Sannan kuma sarakunan Arewa da dama shi suke so ayi wa sarkin na Zazzau.

Magajin Gari Ahmed Bamalli

Magajin Gari Ahmed Bamalli, Ɗan marigayi magajin garin Zazzau Nuhu Bamalli ne.

Ahmed Bamalli na daga cikin wadanda ake ganin ko shi ne dai ko Yerima Mannir za a nada sabon sarki.

Wasu abubuwa da za su yi wa magajin gari Ahmed Bamalli tasiri a wannan lokaci shine kusantar sa da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Da farko dai Ambassada Bamalli ɗan uwa ne ga gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Baya ga haka kuma akwai zumunta na jini a tsakanin su.

Ahmed Bamalli na da gogewa a harkar aikin gwamnati, natsuwa ga shi kuma basarake.

Sannan kuma shine kadai daga cikin neman darewa kujerar sarautar Zazzau da mahaifinsa bai yi sarautar Zazzau ba.

Duka sauran ƴaƴan sarakunan dake nema wannan kujera iyayen su sun yi sarautar Zazzau.

Gwamnati

Gwamnatin jihar Kaduna bata ce komai ba game da wannan dambarwar sarauta da ya kanannade ƴaƴan sarakunan Zazzau ba, sai dai wani jami’in gwamnati da ya ne mi a sakaye sunan sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu ba a kawo sunayen wadanda masu zaben sarki suka zaba fadar gwamnatin jihar ba.

Sai dai kuma ya ce gwamnati zata nada wanda ya fi dacewa ne kuma kila wanda ma ba a yi zaton shine za a nada ba.

Baya ga su akwai Iya Bashar Aminu, wanda shima yana neman sarautar, Sa dai an fi yi masa ganin nasara idan da a tsohuwar gwamnatin da ta wuce ne.

Shima mahaifinsa ya yi sarautar Zazzau.

Daya daga cikin ƴaƴan sarkin mai rasuwa, marigayi Shehu Idrisu, Aminu Idris, shima yana muradun yaga ya gaji mahaifinsa.

Yanzu dai komai ya rage wanda gwamnan Kaduna ya kwanta masa a rai, wanda zai kare masa muradin sa da ci gaban gwamnatin sa, Zazzau da Kasa baki daya.

Share.

game da Author