Masana za su yi wa Boko Haram fidar biri-har-wutsiya a taron gabatar da littafi kan matsalar Boko Haram

0

Shekaru 11 kenan, amma har yau tambayar da ke bakin mutane ita ce, shin wane irin karfi ne Boko Haram ke da shi, har suka sha gaban Sojojin Najeriya da na Kamaru da na Chadi, har ma da wasu daga burbushin sojojin babbar kawar wadannan kasashe, wato Amurka?

‘Yan Najeriya ba su ma ko iya kirga sau nawa gwamnatin Buhari da ta Goodluck Jonathan su ka sha cewa sun murkushe Boko Haram.

Sau da yawa sai bayan gwamnati ta fito ta na fankamar murkushe Boko Haram, sai ‘yan ta’addar su fito su karyata gwamnati, ta hanyar kai wani mummunan hari cikin jama’a.

Yayin da adadin wadanda Boko Haram suka kashe ke kara yawa, har sun kai mutum 27,000 tare da tarwatsa gidajen mutum milyan 2 da kuma laatai dukiyoyi da gine-gine na naira bilyan 17, kamar yadda wasu masana suka yi kintace, to haka kuma gano matsalar rashin tsaron ke kara cukuikuyewa.

Ya zuwa 2019, an buga litattafai sama da 27 a kan Boko Haram.

Cikin wadannan litattafai da ake tattauna “Boko-Haramci”, an buga wasu littattafai uku: Akwai “Sects & Social Disorder”, sai “Creed & Grievance”, da kuma “Overcoming Boko Haram”. Wato a Hausance, “Tasirin Ra’ayin Rikau” “Tsattsaurar Akidar Ruruta Fitintinu” da kuma “Hanyoyin Dakile Boko Haram”.

An fara buga littafi na farko cikin 2014 sai kuma a cikin 2018 aka buga na biyu.

Dakta Mustapha ya yi shirin fito da littafi na cikin 2020, sai ciwon ajali ya same shi a cikin 2017.

A kan haka ne Dakta Kate Meagher ta karasa aikin littafin har aka samu nasarar fitar da littafin a kasuwa cikin watan Fabrairun da ya gabata.

PREMIUM TIMES ta samu alfarmar buga littattafan biyu a Najeriya, kuma aka kaddamar da guda biyu cikin watan Agusta, 2018.

Saboda matsalar Coronavirus, za a gabatar da littafin na 3, wato “Hanyoyin Dakile Boko Haram” ta tsarin taron daga-nesa, a ranar 19 Ga Agusta, karfe 5 na agogon Najeriya, 3:00 na agogon GMT.

Dakta Kate Meagher da Farfesa Kyari Mohammed da Abdourahmane Idrissa da kuma Dakta Fatima Akilu duk za su halarta, ko kuma a ce za su shiga cikin tattaunawa.

Za a fadada tattaunawa jawabai daga abinda littafi ya kunsa zuwa tattaunawa da nazarin matsalar Boko Haram, yadda za a yi wa kungiyar da mummunar akidun ta cakarkaca, a feta ta daga biri har wutsiya.

Wanda zai rika bibiyar sharhin masu nazari sun hada darakta a littattafan da PREMIUM TIMES ke wallafawa, kuma Shugaban Ofishin wannan jarida da ke Amerika, Ladi Olorunyomi.

Share.

game da Author