Majalisar Kasa za ta Kara duba dokar inshoran lafiya na kasa domin saka mata masu shayar da jarirai nonon a cikin shirin.
Majalisar ta ce yin haka zai taimaka wajen wayar da kan mata da sanin muhimmancin shayar da jariran su nonon domin inganta lafiyar su a kasar nan.
Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar Ibrahim Oloriegbe ya sanar da haka a taron tunawa da mahimmancin shayar da jarirai nonon uwa da kungiyar ‘Save the Children International’ ta yi a Abuja.
Idan ba a manta ba a taron sanin mahimmancin shayar da jariri nonon uwa na 2020 ne Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun UNICEF suka yi kira ga gwamnatocin duniya da su cigaba da wayar wa mutanen kasashen su kai game da mahimmancin shayar da jarirai nono na tsawon akalla watanni shida bayan haihuwa.
Shugabanin UNICEF Henrietta Fore da na WHO Tedros Ghebreyesus sun ce shayar da jariri nonon uwa na da mahimmanci matuka suna masu cewa nonon uwa na dauke da sinadarin inganta kiwon lafiyar jariri musamman na kariya daga kamuwa da cututtukan dake kisan yara kanana.
Shugabannin sun ce yin haka zai taimaka wajen ceto rayukan yara akalla 820,000 dake mutuwa duk shekara a duniya.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 bisa 100 na jarirai ne ake shayarwa nonon uwa na tsawon watanni shida a Najeriya.
Rashin yin haka na daya daga cikin dalilan dake kara yawan mace-macen yara da mata a kasar nan.
Shayar da yaro ruwan nono zalla na tsawon watanni shida hanya ce dake taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro da na uwa.