Da gaske ne hukumar FDA ta Amurka ta amince a rika yin maganin Korona da hydroxychloroquine? – Binciken Dubawa

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Amurka, FDA ba ta bayar da umarnin a rika amfani da maganin hydroxychloroquine a matsayin maganin warkar da kwayoyin Korona ba.

Hakan ya biyo bayan wani bincike mai zurfi da shafin DUBAWA ta yi domin tantance sahihancin wannan magana da ake ta yadawa a baya.

An rika yadawa a shafin sada zumunta ta Whatsapp cewa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, FDA, ta amince a rika amfani da magungunan hydroxychloroquine, zinc, da Zithromax don warkar da kwayoyin cutar Korona a jikin mai fama da cutar.

Sakamakon binciken da DUBAWA ta yi ya nuna cewa wannan magana ba gaskiya bane. Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka, FDA, ba ta ce maganin hydroxychloroquine, zinc, da Zithromax na warkar da Korona ba.

Cikakken Bayani

An gano cewa wannan magana da ake ta yadawa ya samo asaline daga wani rubutu da aka yada wai wani likita ne mai suna Dr. Zev Zelenko ya ce a rika amfani da maganin sannan wai har ya fadi yadda za a rika shan maganin kamar haka, Hydroxychloroquine (200mg, sau biyu a rana, na tsawon kwana biyar), Azithromycin (500mg, sau daya a rana, na tsawon kwana biyar) da Zinc Sulphate (220mg, sau daya a rana na tsawon kwana biyar) duk wai idan aka yi haka za a warke daga Korona.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan barkewar annobar Korona a duniya ake ta bayyana wasu hanyoyi da magunguna da ba a tabbatar da tasirun su ba cewa wai suna warkar da cutar. Hakan bai tabbata ba domin hatta hukumar kiwon Lafiya ta duniya ta bayyana cewa babu maganin cutar hanyanzu.

Haka kuma a dalilin haka ko a Najeriya hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa, NAFDAC a Yuli, ta shaida cewa maganin PAXHERBAL CUGZIN baya warkar da Korona.

An samu tabbacin cewa hatta hukumomin kiwon lafiya, Gwamnatoci, kwararru wato masana magunguna sun karyata cewa magungunan hydroxychloroquine, zinc, da kuma da Zithromax na warkar da Korona.

Binciken DUBAWA

Sakamakon bincike da DUBAWA ta yi ya karyata zance da aka rika yadawa da aka jingina ta ga wani likita da aka ce wai ya tabbatar da ingancin cewa wadannan magunguna suna warkar da Korona, sannan kuma bincike da DUBAWA ta yi a shafin FDA, ba a samu inda hukumar ta taba wallafa cewa wai wadannan magunguna na warkar da Korona ba ko kuma wani wuri da ta amince a rika amfani da wadannan magunguna wajen warkar da masu fama da Korona. Hasali ma hukuma FDA gargadi ta yi wa mutane da kada su kuskura su yi amfani da wannan magani.

A karshe kuma ita kanta hukumar Lafiya ta duniya ta gargadi mutanen da ke amfani da magungunan da su gaggauta dakatar da haka.

A takaice dai Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Kasar Amurka, FDA, ba ta taba cewa a rika amfani da magungunan hydroxychloroquine, zinc da Zithromax don warkar da cutar Korona, wato Covid-19 sannan kuma babu wani gwaji da ya tabbatar da ingancin cewa wadannan magunguna suna warkar da kwayoyin utar Korona.

Share.

game da Author