Kiran Kawowa Yankin Arewa Dauki! Daga Imam Muhammad

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwa na masu daraja, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kadai, mahaliccin kowa da komai, mai kashewa, mai rayawa, cewa, nayi binciken gani da ido, nayi yawo, na zagaye jihohin arewa goma sha tara, na gana kuma na tattauna da matasa gaba-da-gaba, ido-da-ido, na shiga cikin matasan mu, naci abinci tare da su, munyi fira, naji ta bakin su, na gano cewa lallai abun da ya jawo, ko kuma yake jawo kashe-kashe, da ayukkan daba, da ayukkan ta’addanci, da ayukkan barna da sauran ayukkan hare-hare da ke faruwa a yankunan arewa, shine kamar haka:

1. Barin dimbin matasan mu a yankin arewa cikin duhun jahilci da rashin ilimi.

2. Barin matasa cikin damuwar rashin abin yi, wato rashin aikin yi.

3. Wasu ‘yan siyasar mu a yankin arewa suna bayar da gudummawa sosai wurin lalata matasan mu, tare da jefa su cikin ayukkan daba da ta’addanci. Saboda suna yi masu aikin cin mutuncin abokan adawar su na siyasa! Kwanan nan wani bidiyo ya nuna wani dan siyasa a jihar Kano yana umurtar ‘yan dabar sa, yaran sa, yana cewa: NI NACE KU KASHE! Yanzu wannan dan siyasa wane mataki za’a dauka a kan shi? Allah kadai ya sani! To ire-iren wadannan suna nan da yawa. Kullun muna ta kukan rashin tsaro a arewa, alhali wasu ‘yan siyasa ne ke bata ‘ya ‘yan talakawa, suna mayar da su ‘yan ta’adda, saboda rashin imani da tsoron Allah. Aikin da ba zasu iya sa ‘ya ‘yan su ba, amma suna sa ‘ya ‘yan talakawa. Suna lalata masu rayuwa. To idan muna son zaman lafiya, wallahi sai an magance wannan!

4. Yin watsi da sha’anin ‘yan uwan mu fulani, wadanda suke zaune a ciki daji, da rugage. An bar su babu ilimin addini da na zamani, tare da rashin kula da su wurin kai masu abubuwan more rayuwa da sauran su. Sannan da ikirarin da wasu fulanin suke yi na cewa suna daukar fansa ne akan zaluntar su da ake yi.

5. Nesantar juna da ake yi, da kyamatar juna, ko kuma haifar da babbar tazara tsakanin masu hali da talakawa. Wannan ya jawo talakawa suke kallon masu hali a matsayin wadanda ke zaluntar su, ko kuma suke yi masu kallon cewa suna da hannu wurin jefa su cikin halin da suke ciki na damuwa da kuncin talauci. Su kuma masu hali suna kallon talakawa a matsayin marasa amfani.

6. Irin yadda manya da ‘ya ‘yan su da iyalan su, suke rayuwa irin ta fantamawa da jin dadi, talakawa suna ji kuma suna kallon su, wannan sai ya jawo aka wayi gari, matasan mu suna hassadar manyan mutane da ‘ya ‘yan su.

7. Yawancin abun da masu mulki ko gwamnatoci suke bayarwa, ko suke fitarwa a raba wa talakawa, ko ayi ma talaka, wallahi baya kai wa ga hannun su. Wadanda ake ba wa hakkin rabon, su suke handame komai, sai a wayi gari talaka bai ma san anyi ba, sai dai yaji labari. Don haka sai gwamnatoci su rinka ganin suna yi, amma talakawa kuma a daya gefen suna ganin ba’a yi masu komai.

8. Mummunar dabi’ar nan ta hadama, da handama da babakere da wasun mu suke da ita. Mutum daya sai a wayi gari ya handame abun da dubban mutane zasu iya amfana da shi!

9. Sannan bincike na ya gano man cewa wasu miyagu, makiyan yankin arewa, wadanda basu son yankin yaci gaba, basu nufin mu da alkhairi, masu son su haddasa muna fitintinu a yankin mu, domin muyi ta kashe junan mu, muna kone dukiyoyin mu, sun ci nasara wurin haddasa gaba, kiyayya, hassada da rashin jituwa, tsakanin ‘yan uwan juna, wato Hausawa da Fulani. Da kuma tsakanin makwabtan juna, wato tsakanin Kiristocin arewa da Musulmin arewa. Don haka ya zama wajibi abi hanyoyin da duk suka dace, masu inganci, domin yin kyakkyawan sulhu, mai dorewa. Ba irin sulhun nan na cuwa-cuwa ba, wanda baya zuwa ko’ina!

Saboda haka wannan kadan kenan daga cikin abubuwan da bincike na ya gano man. Sannan ina kira ga manyan mu na arewa da dukkanin masu ruwa da tsaki wurin mulkar jama’ah a yankin mu, da su yi kokarin duba wadannan al’amurra da idon basira. Domin a gaskiya, tsakanina da Allah, maganar jami’an tsaro kawai, ba zai taba yin maganin matsalar rashin tsaro a arewa ba. Kuma ina mai jawo hankalin ku, da ku san da cewa, muna da babbar matsala a yankin arewa, matasa sun yi yawa, babu sana’a, babu aikin yi, babu ilimi da sauran su. Shi yasa duk wata kungiya ta ta’addanci take samun gindin zama, kuma take samun dimbin mabiya a arewa. Na rantse da Allah, akwai Jihar da na tafi, wasu matasan Jihar suka shaida man cewa, su wallahi a shirye suke, duk tafiyar da tazo, in dai har za su samu mafita daga halin kuncin da suke ciki, zasu shiga ayi da su, tun da basu da masu taimaka masu.

Gwamnatin tarayya da wasu jihohi, sun mayar da hankali sosai wurin sha’anin cutar annobar korona, amma ina mai tabbatar maku, binciken da nayi, ya tabbatar man da cewa, a arewa sam ba’a ma yarda da cewa wannan cuta akwai ta ba. ‘Yan boko ne kawai, da jam’ian gwamnati suka yarda da wannan cuta a arewa. Amma ina mai tabbatar maku da cewa, wallahi mafi yawan talakawan arewa basu yarda da ita ba. Duk mai ya kawo wannan? Kawai rashin yarda ne tsakanin masu mulki da talakawa!

Don haka ni dai nayi nawa aiki, kuma na fada maku gaskiya tsakanina da Allah, cewa muna da matsala a yankin mu mai albarka na arewa. Yanzu haka na gama zagayen da nike yi, gani a cikin gari na, wato garin Gusau a jihar Zamfara. Kusan kullun sai an kai hari wani wuri a jihar Zamfara, sai kaji an kashe wani ko wasu. Jiya wallahi aka karbo wani dan uwan mu mai suna YAHAYA daga hannun masu sace mutane, bayan an biya kudi, anan Gusau.

Ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin mu na arewa da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar shugabanci ko harkar tsaro, da su san da cewa wallahi arewa fa babu lafiya, sannan kuma akwai matsalar da idan ba’a yi kokarin magance ta ba, to ina tsoron abun da zai faru nan gaba… Allah ya tsare, amin.

Daga karshe, ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kawo muna karshen wadannan matsaloli da ke faruwa a arewa da ma Najeriya baki daya, Allah ya taimaki Shugabannin mu, ya basu ikon samun mafita daga wannan matsala, amin.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau. 08038289761.

Share.

game da Author