Mahara dauke da makamai sun datse Titin da ya ratsa ta dajin Falgore dake ƙaramar hukumar Doguwa, Jihar Kano inda suka yi garkuwa da wasu matafiya Uku.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa wani da abin ya auku a gaban sa ya bayyana cewa cikin wadanda suka ji rauni a wannan hari har da shugaban ƙungiyar Hisbah na ƙaramar Doguwa, Mukhtar Abdulmumini.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar wannan hari sanna ya ce tuni har jami’an ƴan sanda sun fantsama domin farautar wadannan masu garkuwa da mutane.