Kamfanonin Hada Magunguna Sun Koka Kan Rashin Isa Ga Biliyan 100 Da CBN Ta Ware Musu

0

Kamfanoni hada magunguna ta kasa ta koka kan rashin iya cimma asusun da aka jibge biliyan 100 da Bankin Kasa, wato CBN ta samar domin yin bincike da hada magunguna musamman a wannan lokaci na Korona.

Kungiyar masana magunguna ta Najeriya PSN ta bayyana cewa Kamfanonin sarafa magunguna na kasar nan basu iya kaiwa ga kudaden da babban bankin Najeriya CBN ta ware domin dalike yaduwar cutar Korona a kasar nan.

Bankin CBN ta ware Naira biliyan 100 domin rabawa Kamfanonin dake hada magunguna su yi amfani dasu wajen yin bincike da hada magani a wannan lokaci da kasashen duniya ke kokarin kirkiro rigakafin annobar Korona.

CBN ta ware wannan kudade tun daga watan Maris din 2020.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 138 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 15, Filato-55, Ebonyi-11, Oyo-11, Abia-8, Anambra-7, FCT-7, Rivers-7, Kaduna-6, Ondo-5, Kwara-3, Bauchi-1, Benue-1, da Edo-1.

Yanzu mutum 53,865 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 41,513 sun warke, 1,013 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,339 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,188 , FCT –5,156, Oyo – 3,118, Edo –2,578, Delta –1,744, Rivers 2,141, Kano –1,725, Ogun – 1,646, Kaduna –2,120, Katsina –789, Ondo –1,539, Borno –740, Gombe – 723, Bauchi – 667, Ebonyi – 984, Filato -2,429, Enugu –1,155, Abia – 771, Imo – 527, Jigawa – 322, Kwara – 961, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 779, Sokoto – 158, Niger – 241, Akwa Ibom – 278, Benue – 452, Adamawa – 221, Anambra – 214, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 262, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.

Share.

game da Author