Ghana ta ce ta nuna damuwa sosai dangane da jawabin da Ministan Yaɗa Labarai na Najeriya, Lai Mohammed ya yi, a ranar 28 Ga Agusta, 2020, a madadin Gwamnatin Najeriya.
Yayin da Ghana ta ce ba za ta taba bari dangantaka tsakanin ta da kasashe makauta ko makusanta irin su Najeriya ta yi tsami ba, duk da haka ta ce akwai bukatar ta fito ta bayyana dalla-dalla yadda al’amarin ya kawo ja-in-ja tsakanin Gwamnatin Ghana da Najeriya a kan wasu muhimman batutuwa:
1. Zargin Kwace Ofishin Jakadancin Najeriya:
Wannan ofishi da ke kan titin Barnes Rosol, Lamba 10 a Accra, tsawon shekaru 50 kenan Najeriya na amfani da shi. To a gaskiya ya kauce wa ka’idar Taron Duniya na Vienna.
Matsalar Da Ke Tattare Da Ofishin:
Najeriya ta karbi hayar ginin a hannun wani ejan mai suna Thomas D. Hardy, a Ghana, tun a ranar 23 Ga Oktoba, 1959.
Yarjejeniyar karbar hayar ta kare shekaru 46 da suka wuce, kuma babu wata takarda da ke nuna cewa Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Ghana sun sabunta ko sun taba sabunta jarjejeniyar karbar hayar. Saboda haka wannan gini ba mallakin gwamatin Ghana ba ne. Babu ruwan Ghana da rikicin, sannan kuma ba ta kwace shi daga hannun Ofishin Jakadancin Najeriya ba.
2. ZARGI NA BIYU:
Gwamnatin Ghana ba ta da hakkin mallakar filaye. Kuma ba ita ce ta kwace ginin daga hannun Ofishin Jakadancin Najeriya ba. Wanann wuri mallakar Osu Stool ne, wadda sarautar gargajiya ce.
Sannan da ake yi wa kasar Ghana gori cewa ita ma wa’adin zaman Ofishin ta na Abuja ya dade da wucewa, amma ba a kore su ba, to Ghana ta samu fili ne a Abuja a kan titin Pope John Paul II, tun a cikin 1989. Kuma ta yi gini a cikin filin.
Kuma ma’aikatan Ofishin Jakadancin Ghana da ke Abuja, a cikin ginin suke zaune tun tuni ba tun yau ba.
3. Zargin Rushe Ginin Ofishin Jakadancin Najeriya Da Ke Lamba 19/21, Titin Julius Nyerere.
Wannan zargi ba gaskiya ba ne. Bayan an bai wa Ofishin Jakadancin Najeriya filin cikin shekarar 2000, sai Ofishin ya kasa mallakar takardun hakkin mallakar satifiket. Ba ejan din gwamnati ne suka rushe ginin ba. Ejan din Gidan Sarautar Osu ne suka rusa ginin.
4. Zargin Ghana ta kori ƴan Najeriya 825 tsakanin Janairu 2018 zuwa Fabrairu 2019.
Wannan ba gaskiya ba ne. Amma cikin 2019 Ghana ta kori ƴan Najeriya 700, waɗanda aka kama da aikata muggan laifuka daban-daban, kamar fashi da makami, damfara da karuwanci.
5. Zargin Tsawwala Wa Ƴan Najeriya Kuɗin Takardun Iznin Zama Cikin ƙasa.
Wannan ƙarya ce, ba gaskiya ba ne. Kuɗin da Hukumar Shige-da-fice ta Ghana ke cajin ƴan Najeriya, ba shi da bambanci da abin da ta ke cajin kowane ɗan kasa a duniya. Kuɗin duk ɗaya ne.
6. Zargin Gidajen Jaridu na bata wa ƴan Najeriya mazauna Ghana suna, har ana nuna musu ƙiyayya, kamawa da kulle musu shaguna da kantina.
Wannan ma ba gaskiya ba ne. Babu yaƙin ɓata suna da jaridun Ghana ke wa ƴan Najeriya. Kuma babu inda ake tsanar su ko ko kama su.
Duk wani shago da aka kulle, ko ma na wa ne ne, to doka ya karya. Doka kuma ta na hawa kan dan kasa ko bako, in dai ya karya ta.
7. Zargin Kotunan Ghana Na Tsaurara Wa Ƴan Najeriya Hukunci Da Nuna Bambanci.
Wannan ma ba gaskiya ba ne. Dukkan kotunan Ghana zaman kan su su ke yi. Kuma ba su nuna bambanci ga yanke hukunci. Duk wani hukuncin da suka yanke akwai kwafe a ajiye da za a iya bincika a tabbatar.
8. Zargin Yi Wa Dokar GIPC Kwaskwarima:
Wannan ba gaskiya ba ne. Ghana ba ta yi wa wata doka kwaskwarima har sau biyu ba. Hasali ma babu wata Dokar GIPC ta 2018.
Abubuwa da dama sun bijiro sakamakon yadda masu kantina da shaguna ke karya dokoki. Kuma ba ƴan Najeriya ne kaɗai ba. Akwai ‘yan cikin kasar Ghana da sauran kasashe da yawa. Akwai kin biyan haraji, sayar da kayan jabu, sayar da kaya marasa inganci, amfani da takardun jabu da sauran laifukan da doka ba za ta iya kauda kai ba.
A karshe Ghana na neman hadin kan Najeriya da sauran ƙasashen ECOWAS domin ganin wannan yanki ya ci gaba da kuma bunkasa.