Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 601 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 404, FCT-37, Oyo-19, Ondo-14, Abia-13, Enugu-13, Kaduna-13, Edo-12, Kano-12, Kwara-11, Ebonyi-10, Nasarawa-7,Ogun-6Osun-5, Delta-5, Niger-5 Filato-4, Bayelsa-4, Katsina-3, Ekiti-2 da Imo-2
Yanzu mutum 51,905 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 38,767 sun warke, 997 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,141 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,764 FCT –4,969 , Oyo – 3,036, Edo –2,520, Delta –1,701, Rivers 2,048, Kano –1,704, Ogun – 1,600, Kaduna –1,999 Katsina –771, Ondo –1,501 , Borno –739, Gombe – 709, Bauchi – 607, Ebonyi – 957, Filato -2,113, Enugu – 1,043, Abia – 739, Imo – 521, Jigawa – 322, Kwara – 931, Bayelsa – 356, Nasarawa – 396, Osun – 762, Sokoto – 156, Niger – 237, Akwa Ibom – 271, Benue – 430 , Adamawa – 206, Anambra – 181, Kebbi – 90, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 218 , Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 80.
Kasashe 24 da Korona bata kashe koda mutum daya ba har yanzu
A tsawon watanni bakwai da bayyanar cutar Korona akalla mutum sama da mutum milyan 20 ne a duniya suka kamu da kwayoyin cutar kamar yadda rumbun adana alkaluman kididdigan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona mai suna worldometers.info ya bayyana.
Cutar ta yadu zuwa kasashe sama da 200 sannan ta kashe mutum sama da 750,000.
Sakamakon binciken ‘worldometers’ ya kuma nuna cewa akwai wasu kasashe a wannan duniya ta mu har 24 da duk da cutar ta kai gasu amma babu koda mutum daya ne da ya rasu a dalilin kamuw ada ita.
Ga jerin Kasashen a nan:
1. Kasar Tsibirin Faroe, Faroe Islands
A wannan kasa dake da yawan mutum 50,000 mutum 339 aka samu sun kamu da kwayoyin cutar Korona. Gwamnatin kasar ta yi wa akalla kashi 40% na mutanen kasar. Har yanzu babu wanda ya rasa rai a dalilin wannan cuta.
2. Kasar Mongolia
Kasar Mongolia na da Iyaka da kasar Chana amma har yanzu babu wanda cutar ta yi ajalisa a kasar.
Mutum 293 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 269 sun warke. Mutum 24 ke kwance a asibiti a kasar babu mutuwa ko daya.
Zuwa yanzu gwamnatin kasar ta yi wa mutum 41, 584 gwajin cutar daga cikin ‘yan kasan mutum sama da miliyan uku.
3. Kasar Eritrea
A kasar Eritrea wanda tana yankin Afrika ne, mutum 285 suka kamu da cutar tun bayan barkewarta. Zuwa yanzu mutum 248 sun warke. Babu mutuwa.
4. Kasar Cambodia
Akalla mutum 75,000 ne aka yi wa gwajin cutar cikin mutum miliyan 16 a kasar Cambodia.
5.Kasar Gibraltar
Sakamakon binciken ‘worldometers’ ya nuna cewa kwayoyin mutane suka kamu da cutar a kasar cinkin ‘yan kasa 33,000.
6. Kasar Seychelles
‘Yan Kasa 100,000, mutum 127 suka kamu, 126 sun warke. Babu mutuwa ko daya.
7. Kasar Bhutan
Cikin ‘yan kasar mutum sama da 800,000 mutum 113 suka Kamu, babu mutuwa
8. Kasar French Polynesia
Cikin ‘yan kasa 280,000, mutum 112 suka kamu da cutar. Babu mutuwa ko daya.
9. St. Vincent and the Grenadines
Cikin ‘yan kasa 110,000 mutum 57 sun Kamu, 52 sun warke. Babu mutuwa ko daya.
10. Macao
Cikin ‘Yan kasa 650,000, mutum 46 ne suka kamu da Korona kuma duka sun warke. Babu mutuwa ko daya.
11. Saint Lucia
Cikin ‘Yan kasa 183,723, mutum 24 ne suka kamu. Babu mutuwa ko daya.
12. Timor-Leste
Cikin ‘yan kasa miliyan 1,321,156, mutum 25 ne suka kamu, babu wanda ya rasu.
13. Grenada
Cikin ‘yan kasa 112, 583, babu wanda ya rasu cikin kalilan din da suka kamu.
Sauran sun hada da:
14. New Caledonia
15. Laos
16. Dominica
17. Saint Kitts da Nevis
18. Greenland
19. Caribbean Netherlands
20. Falkland Islands
21. St. Barth
22. Vatican City
23. St. Pierre Miquelon
24. Anguilla