‘An ci wa El-Rufai mutunci saboda dan Arewa ne’, Kungiyoyin Lauyoyin Yobe, Bauchi, Jigawa da na Musulmai sun janye daga halartar taron NBA

0

A cigaba da samun goyon bayan kungiyoyin Lauyoyi na jihohin kasar nan da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ke ta samu, kungiyoyin lauyoyi reshen jihohin Bauchi da Yobe da kuma kungiyar Lauyoyi Musulmai na reshen jihar Kaduna duk sun bayyana cewa baza su halarci taron kungiyar ta Kasa da za a yi a mako mai zuwa ba.

Tun bayan dakatar da gwamnan jihar Kaduna daga yin jawabi a ataron kungiyar bayan ta gayyace shi, mutanen Najeriya da dama suka rika tofin Alla tsine ga kungiyar da nuna rashin jin dadin su.

Tun a lokacin da kungiyar ta yanke hukuncin cire sunan sa daga masu halartar taron, kubgiyar reshen jihar Jigawa ta fito karara domin sukar kungiyar.

Mambobin da suka fusata da dakatar da gwamnan Kaduna daga halartar taron sun ce abinda kungiyar tayi nuni ne da adawa da gwamnan don yana dan Arewa domin akwai gwamnan jihar Ribas wanda ya fi kowani gwamna tabargaza a wannan kasa amma shi an bashi dama don dan kudu ne, sai Nasir El-Rufai suka tsana.

Kungiyoyin sun koka cewa uwar kungiyar bata yi wa gwamna NAsiru adalci ba domin kuwa bayan iat da kanta ta gayyace shi amma kuma kwatsam a rana tysaka don wasu tsiraru sun nuna basu son shi sai kawai a dakatar dashi.

Yanzu dai ana samun karin wasu jihohi da dama suna nuna goyon bayan su ga El-Rufai da nuna adawa ga kungiyar Lauyoyin.

Idan ba a manta ba, shi kansa shugaban Kungiyar Paul Osaro ya roki yafiyar gwamnan yana mai cewa, kwamitin gudanarwar kungiyar ne suka ki amincewa ya yi jawabi a taron.

Share.

game da Author