Mahara sun kashe mutum 15 a jihar Katsina

0

Akalla mutum 15 ne mahara suka kashe a kauyen Ruma dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina ranar Litini.

Hakimin Batsari Tukur Mu’azu ya Sanar da haka wa PREMIUM TIMES, yana mai cewa maharan sun far wa kauyen lokacin da mutane sun garzaya gonakinsu dake ‘yar Gamji wajen garin Batsari.

Hakimin kauyen ya ce wannan harin ya auku ne bayan an yi shekara daya da wasu mahara suka far wa kauyen.

Ya ce a wannan hari maharan sun kashe mutum 18 a kauyen Ruma.

A yanzu mutum biyu sun bace a dalilin harin da aka yi ranar Litini.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isah bai ce komai ba game da harin ranar Litini.

Wannan harin ya auku duk da kokarin fatattaka ‘yan ta’adda da jami’an tsaro ke yi a Arewa maso Gabas.

A ranar Litini ne Shugaban rundunar sojin Najeriya Tukur Buratai ya kaddamar da ‘Operation Sahel Sanity’ a karamar hukumar Jibia domin kawar da kashe-kashen mutane da ake yi a jihar.

Hakimin kauyen ya ce maharan sun far wa kauyen ne yayin da jami’an tsaro ke Zama.

Ya ce ga dukan alamu wadannan mahara na son manoma su koma gida ne kawai bana.

Share.

game da Author