Farfesa Cyril Otoikhian na jami’ar Novena dake jihar Delta ya karyata annobar Korona, cewa babu wata kwayar cuta Korona da ake ta yayadawa a duniya.
Farfesan ya kalubalance malaman kimiya, likitici da gwamnatin Najeriya su karyata shi ta hanyar nuna wa mutane kwayar cutar idan da gaske ne.
Farfesan ya ce ko gwajin cutar da bayyanata a mynafunce ake yi ba a so kowa ya sani, cewa hakan ya na tabbatar da cewa babu wannan cuta ne, kawai farfaganda ce a Najeriya.
Da shugaban AIT ya warke da ga cutar, ya shaida cewa babu marabar cutar da zazzabin cizon Sauro.
Shi kan sa mai yi masa tambaya ya fada cukin rudani gwanin wannan mutum dai farfesa sanin kwayoyin halitta ne ya ke karyata wannan cutar.
” Kun ce akwai cuta wai Korona, amma kuma ba ku taba nuna mata ita ba. A bayyana ta karara duka kwararrun kimiyya su garzayo a baje ta a faifai, yan jarida su zo suma da kamarorin su a fede biri daga kai bindi. Amma kuma ba haka ake yi ba yanzu.
” Na kalubalance su su kawo min mutum da aka ce ya kamu da cutar Korona da wanda ma ya mutu a sanadiyyar cutar. Za mu gudanar da bincike daki-daki daga nan sai a nuna min menene Korona a jikin su wanda ke rayen da Koronan da ta kashe wanda ke kwance. Duk rude akr yi kawai
Sai dai kuma wani likitan sani da binciken kwayoyin cuta, Akayala Ishaku, ya karyata Farfesa Cyril, in da yace kwarewar da ta banza ce idan miliyoyin hujjojin da ke yawo a duniya kan cutar bai iya gamsar da shi.
” Cyril na ganin haka kawai idan ba din cuta irin Korona ba kasashen duniya za su garkame kasashen su a yi ta hasarar biliyoyin kudi haka kawai.