Gwamnan Delta da matar sa sun kamu da Korona

0

Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa shi da matar sa sun kamu da cutar Coronavirus.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar da kan sa, a shafin sa na Facebook, ya sanar cewa ita ma matar sa Edeth Okowa ta kamu da cutar.

Ya buga wannan sanarwa ce a Laraba din nan da safe.

“Ni da mata ta duk mun kamu da cutar Coronavirus. Amma dai lafiya kalau mu ke, babu abin da ke damun mu. Sai dai kawai mu na ci gaba da killace kan mu. Mu na godiya ga dimbin masoya masu yi mana addu’a, mu da ‘yar mu, wadda ita ma ta kamu da cutar, kuma tuni ta ke a killace.”

Dama tun cikin makon jiya ne Okowa ya killace kan sa, bayan gwaji ya nuna cewa wata daya daga cikin ‘ya’yan sa ta kamu da cutar.

Kakakin Yada Labaran Okowa, Olisa Ifeajika ne ya sanar da kamuwar ‘yar gwamnan, wanda ya ce tuni aka killace ta tsawon kwanaki 14.

Bayan an an samu Sakataren Gwamnatin Jihar Bayelsa, Chiedu Ebie da cutar Coronavirus, shi da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Charles Aniagwu.

Ranar Talata PREMIUM TIMES ta buga labarin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar Coronavirus.

Tuni Rotimi ya killace kan sa, tare sa bada umarnin tilas a yi wa dukkan kwamishinonin sa, mukarrabai da sauran ma’aikatan gidan gwamnatin Ondo gwaji, domin a tantance barcin-makaho.

Zuwa yanzu gwamnoni biyar ne a kasar nan suka kamu da cutar Coronavirus.

Bayan su kuma akwai manyan jami’an gwamnati da dama.

Share.

game da Author