Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.
Cikin wata sanarwa da Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar a taron WHO, ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.
Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.
“Bala’in cutar Coronavirus da mu ke ciki a yanzu, kadan ne ga gagarimin bala’in ta da zai fuskance mu gadan-gadan, nan da watanni kadan masu zuwa.
“Watanni shida baya, babu wanda ya yi tsammanin duniya za ta afka cikin bala’in Coronavirus sa ake ciki a yanzu.
“Kowa na son ganin karshen wannan cuta. Sannan kowa ba son ganin an koma gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda ake kafin bullar wannan cuta. Amma a gaskiyar magana, ba ma kamo hanyar kawo karshen wannan cuta ba.”
Mun Bani Mun Lalace:
Tedros ya ce, babu abin da zai ce, sai dai ya ce, “mun riga mun shiga iyar wuya, ba mu san ranar fita ba.”
Ya ce an yi rashi da yawa a duniya sanadiyyar wannan cuta. Sai dai kuma ya bada kwarin-guiwar cewa, “kada a karaya, a jajirce, a kimtsa, a jure, a tausaya wa jama’a, kuma a rika kyautatawa ta hanyar tallafi da gudummawa.”
Hasashen WHO Cikin Watan Maris:
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labari, a baya inda a ranar 11 Ga Maris, 2020_ ta ruwaito WHO na cewa, “Coronavirus ta zama annobar-ruwan-dare, domin za ta mamaye duniya.”
A lokacin da WHO ta yi wannan hasashen. mutanen da suka kamu da cutar kadan suka haura 118,000 a duniya.
Kuma wadanda cutar ta kashe a duniya a lokacin su 4,000 da kadan ne.
Yadda Korona Ta Tsugunar Da Duniya:
Mutane 41 na farkon da suka ku da cutar, daga birnin Wuhan ta kama su da ke cikin tsibirin yankin gundumar Hubei.
Cutar ta fara bayyana a ranar 10 Ga Janairu, 2020, daga nan kuma ta ci gaba da bazuwa har ta kai cikin kasashe sama da 200 a duniya.
Yayin da milyoyi kan kamu da cutar su warke garas, Coronavirus ta fi kashe masu yawan shekaru a duniya, musamman kuma wadanda ke fama da wani ciwon da ya kwantar da su, ko masu jiyya a tsaitsaye.
Ya zuwa lokacin da ake dubuta wannan labari, an tattara adadin wadanda cutar ta kama a duniya sun kai milyan 10, 590, 953.
Wadanda ta kashe a duniya sun kai mutum 514, 021.
A Amurka ta fi yin mummunan kisa, inda ta ci rayukan mutum sama da 130,000. Yayin da ta kama mutum milyan 2, 727, 853 a Amurka din.
Coronavirus ta fi yin barna a kasashen Amurka, Brazil, Rasha da Indiya, inda a wadannan kasashe hudu ta ci rayukan mutum 514, 021.
A Italy, Spain, France da Rasha ta kashe mutum sama da 150,000.
A nahiyar Afrika kuwa, duk da cewa cutar a hankali da kadan-kadan ta fara fantsama, zuwa yanzu cutar ta kashe sama da mutum 10,000, a nahiya mai al’umma sama da su bilyan daya.
Discussion about this post