KORONA: Kaduna 52, Abuja 52, Kano 5, Yanzu mutum 25,694 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 561 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 200, Edo -119, Kaduna- 52, FCT -52, Niger 32, Ogun 19, Ondo 16, Imo 14, Filato -1, Abia 8, Oyo 8, Bayelsa 7, Katsina 6, Kano 5, Bauchi 3, Osun 3, Kebbi 3, Borno 2, Jigawa 1.

Yanzu mutum 25,694 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 9746 sun warke, 590 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 10,510, daga nan sai FCT – 1,870, Oyo – 1, 380, Kano – 1, 216, Rivers – 1, 056, Edo – 1,105, Delta – 956, Ogun –826, Kaduna – 766, Katsina – 557, Bauchi – 503, Gombe – 503, Borno – 493, Ebonyi – 438, Filato – 382, Jigawa – 318, Imo – 332, Abia – 310, Enugu – 261, Ondo – 292, Kwara – 217, Nasarawa – 213, Bayelsa – 205, Sokoto – 151, Osun – 127, Akwa Ibom – 86, Adamawa – 84, Niger – 116, Kebbi – 76, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 59, Benue – 59, Ekiti – 43, Taraba- 19 da Kogi – 4.

Hukumar NCDC ta gargadi mutane da su kula da tsoffi musamman wadanda ke fama da rashin lafiya kamar Asma, ciwon siga da dai sauran su. Hukumar ta ce likitoci sun shaida cewa lallai irin wadannan tsofaffi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.

Haka zalika, idan ba a manta ba, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru ya shaida cewa jihar ta sallami duka wadanda suka kamu da cutar.

Share.

game da Author