Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun, ta bayyana damke wani matashin fakaneza, wanda ya sace dan kamfan wata mata, bayan ya je ya yi wa tayoyin motar ta faci da gejin iska.
Kakakin ‘Yan Sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a ranar Lahadi.
Ya ce wata mata ce da suka boye sunan ta, ta garzaya Ofishin ‘Yan Sanda na Warewa, ta kai rahoton sace mata dan kamfai.
Ta shaida wa jami’an tsaro cewa ta kira wani mai faci domin yi wa tayar mota faci da kuma gejin sauran tayoyi.
Bayan fitar sa, ya gama gejin, sai ta duba sama ko kasa, ta rasa wani dan kamfai daga cikin kayan wankin da ta shanya a kan igiya, cikin gidan ta.
Matar ta ce, ta tsaya tsaf, ta yi tunanin babu wani wanda ya shiga ko ya fita a gidan ta sai wannanai faci.
Ta ce ta garzaya a wurin da ya ke faci, amma ba ta same shi ba.
“DOP na Ofishin Warewa, Folake Afenitoro, ya baza ‘yan sanda farautar mai facin, kuma su ka yi nasarar damko shi.
“An binciki gidan sa, kuma an bankado inda ya boye dan kamfan matar.”
Kakakin Yada Labarai Oyeyemi, ya ce an tambaye shi abin da zai yi da duros din, sai ya yi ikirarin cewa ya yi niyyar kai shi wajen wani matsafi ne domin a yi masa tsafi da kamfai din, shi kuma ya yi kudin-dare daya, a rana daya ya zama kicima.
Ksamishinan ‘Yan Sandan Ogun Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin a gaggauta gufanar da bakanezan kotu da an kammala bincike.