Wasu ‘yan bindigar da aka hakkake cewa ko dai Boko Haram ne, ko kuma ‘yan bangaren ISWAP ne, sun darkake kauyuka uku cikin Karamar Hukumar Magumeri, su ka kashe mutum biyar, tare da arcewa da shanu 480 a rana daya.
Jami’an gwamnati sun tabbatar da faruwar wannan farmaki wanda aka kai wa mazauna kauyukan Moduri, Kelewa da Ngudori da ke cikin Karamar Hukumar Magumeri, wajen karfe 6:30 na safiyar Asabar.
An ruwaito cewa maharan dauke su ke da zabga-zabgan bindigogin da tarbar gaban su sai da kwakkwaran shiri.
Magumeri ta yi iyaka da Kananan Hukumomin Gubio da Monguno, inda Boko Haram suka kashe mutum 120 cikin ‘yan kwanakin baya.
Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnatin Jihar Barno sun tabbatar da cewa wannan yanki ne mafi zama cikin barazanar Boko Haram da ISWAP a fadin jihar Barno.
Wani jami’in CJTF mai suna Bunu Malam, ya tabbatar wa wakilin PREMIUM TIMES da afkuwar farmakin a kauyukan guda uku.
Shi ma Sakataren Mulkin Karamar Hukumar Magumeri, ya shaida wa manema labarai cewa tabbas an kai hare-haren.
Ali Kyari ya kara da cewa ‘yan bindigar tafe su ke a cikin mummunan shiri, inda suka rika kwasar kayan abinci da kuma shanu. Sun kuma rika bindige wanda ya tare musu gaba da kuma harbin kan-mai-tsautsayi.
“A ranar Asabar lamarin ya faru. Sun fara dira kauyen Maduri, suka kwashi shanu 300, suka kuma bindige mutum 3.
“Sai kuma su ka nausa kauyen Kelewa, inda suka arce da shanu 80, bayan sun kashe mutum daya.
Da su ka dira kauyen Ngudori kuwa, sun arce da shanu 100 kuma su ka kashe mutum daya.
Sakataren Karamar Hukumar Magumeri dai ya yi kira ga jami’an tsaro du kara sa-ido, musamman yanzu da masu gudun hijira ke kokarin sayar da rayukan su su koma gida domin su noma abin da za su ci a daminar bana.
Discussion about this post