Kungiyar Likitoci ta Kasa ta ce ta janye jayin aikin daga Litinin din nan, karfe 8 na safe.
NARD, ta ce ta janye yajin aikin ne bayan manyan kasar nan irin su Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi sun rarrashu, kuma sun yi musu alkawarin cewa ta a gaggauta biya musu dukkan bukatun da suka yi korafin Gwamnatin Tarayya ta ki biya musu, wadanda duk hakkokin su ne, ba alfarma ce su ka nema a yi musu ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda NARD ta ajiye aiki a dukkan manyan asibitocin kasar nan, bayan Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan albashin su, kudaden alawus-alawus da kuma kasa wadatar da su da kayan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus.
Shugaban kungiyar ya ce abin takaici ne kasa biyan alawus, albashi da kuma rashin kula, sannan kuma a kasa wadatar da su da kayan kariya daga cutar Coronavirus da gwamnati bata iya yi ba.
Ya ce kayan kariya daga cutar abu ne da ake bukata a koda yaushe, musamman saboda wasu kayayyakin idan aka yi amfani da su sau daya, ba a karawa, sai dai a canja wasu sabbi kuma.
NARD ta je ta umarci wakilan kungiyar masu tattaunawa da Gwamnatin Tarayya su ci gaba tare da yi su na bada rahoton inda aka kwana da kuma inda za a tashi, nan da makonmi hudu, a cikin watan Yuli.
A na ta bangaren, Gwamnatin Tarayya a fitar da naira bilyan 4.5 domin raba wa Manyan Asibitocin Koyarwa na Jami’o’i da Manyan Asibitocin Gwamnatin Tarayya su 31.
Sannan kuma gwamnati ta amimce da bukatar da Kungiyar NARD ta yi, cewa a fasa korar likitocin da aka sallama a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, tare da biyan su albashin su na watannin Afrilu da Mayu.