KORONA: Mutum 127 suka kamu a jihar, an sallami mutum 88

0

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Filato Lar Ndam ya bayyana cewa mutum 127 suka kamu da cutar coronavirus kuma a cikin su an sallami mutum 88.

Ndam ya fadi haka ne a zaman da kwamitin dakile yaduwar cutar ta yi a jihar ranar Talata.

Ya ce jihar ta yi wa mutum 1,830 gwajin cutar inda daga ciki mutum 127 suka kamu da cutar.

A yanzu haka an sallami mutum 88 sannan 35 na kwance a asibiti.

Ndam ya ce cutar ta yi ajalin mutum biyu a jihar.

“An killace wadannan mutane a asibitin killace masu dauke da cutar inda a nan muka dauki jinin su aka yi musu gwaji.

“Kafin sakamakon gwajin ya fito wasu biyu daga ciki sun tsere daga bata kuma sai aka samu labarin cewa sun rasu a dalilin cutar.

Sannan a yanzu haka gwamnatin jihar ta killace akalla mutane 55 da ake zaton suna dauke da kwayoyin cutar Korona.

Bayan haka shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar dokokin jihar Nanbol Daniel ya yi wa mutanen jihar alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da kula da mutanen da suka kamu da cutar sannan kuma ya kara da yin kira ga mutane su bi dokokin da aka saka na samun kariya daga kamuwa da cutar Korona.

Share.

game da Author