Masana harkokin dabarun noman doya sun shawarci masu dashen iri da masu noman doya kada su dararrashe a gida saboda Coronavirus.
An shawarce su cewa su rika raba aiki, ta yadda idan wannan ya je gona tsawon kwanaki biyu ko uku, sai ya zauna gida, wani Kuma sai ya canje shi, shi ma ya rika zuwa gona tsawon kwanaki biyu ko uku.
Masanan sun ce ta haka be kawai za a iya tabbatar da cewa an samu wadatar abinci ba tare da samun mummunan yankewar abinci ba.
Cibiyar IITA ce ta bayyana Haka a cikin rahoton ta na 2020, wanda aka wallafa a ranar 8 Ga Yuni.
IITA cibiya ce Mai tallafawa wajen kirkiro wa manoma sabbin hanyoyi, dabaru da shawarwararin noma, yadda a za a samu wadatattun kayan abincin da za a kauce wa barkewar yunwa, karancin abinci Mai gina jiki, kuncin rayuwa da sauran matsaloli.
Shugaban Cibiyar Bunkasa Noman Doya a Afrika ta Yamma (YIISFA), Norbert Marcya, ne ya bayyana Haka a wata takaitacciyar tattaunawa da aka yi da shi dangane da makomar noman doya a wannan yanayi da ake ciki na Coronavirus a Najeriya da Ghana.
“Mun bada shawara cewa duk da ana cikin halin Coronavirus, to kada manoman doya baki dayan su su koma gida su zauna ba su kula da gonakin su.
“Kamata ya yi a rika yin aikin karba-karba, yadda yadda a rika samun wanda zai rika kula da dashen doya har tsawon kawana uku akalla.
“Kun ga cutar Coronavirus ta barke daidai lokacin fara dashen doya da noman ta. Saboda haka idan manoma suka yi dirshan a gida, za a rasa wanda zai rika kula da doyar da aka dasa din.”
Sai ya bayyana cewa idan mutum na da gona mai fadin hekta daya, sai ya zauna a gida bai fita aikin dashe da noman doya ba har bayan watanni biyu, to rabin hekta kadai zai iya aikatawa, sauran ba za su yi albarkar noma ba.
Norbert ya bada shawarar cewa manoman doya su rika fits gonaki, amma su rika yin tsarin-karba-karba.
“Su ma wadanda ke zuwa gonar su rika daukar matakan kariya daga Coronavirus, kamar yadda mazauna gida ke yi, ta hanyar yawan wanke hannu da sabulu ko ruwan mai na tsaftace hannu, sanya takunkumi da kuma kauce wa gwamutsuwa cikin tirmitsitsin
jama’a.”
Daga nan ya kara da cewa su na bayar da wadannan shawarwararin ne domin tabbatar da cewa doya a matsayin ta na abinci mai gina jiki ga al’ummar Afrika ta Yamma, ba ta yi karanci nan gaba ba.
Yin hakan inji shi dabaru ne Kuma na hana yunwa yin tasiri a wannan nahiya ta Afrika ta Yamma.