Kotun majistare dake Abeokuta jihar Ogun ta daure wani matashi mai suna Musa Anifowose mai shekaru 21 a kurkuku na tsawon shekaru biyu bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘yar shekara 8 fyade.
Kotun ta yanke wa Anifowose dake zama a Isale Iyemule, Ijebu Ode wannan hukunci ne ranar Laraba.
Alkalin kotun I.O Abudu ta bayyana cewa kotu ta yanke wa Anifowose hukuncin haka ne bisa ga kwararan hujjoji da aka gabatar a gaban kotun wanda suka tabbatar cewa Anifowose ya aikata haka.
Lauyan da ta shigar da karan Bukola Abolade ta bayyana cewa Anifowose ya aikata wannan mummunar abu ne ranar 1 ga watan mayu da misalin karfe 9 na safe.
“Wata rana Anifowose ya gamu da wannan yarinya a lokacin da mahaifinta ya aike ta wani wuri.
“Anifowose ya kama yarinyar da karfi tsiya ya kaita wani kangon gini inda a nan ya danne ta yayi lalata da ita.
” Bayan ta dawo daga aiken sai mahaifiyar ta ta hangi alamun jini a kayanta, sai ta fara binciken abin da ya faru da ita a gidan.