Babbar Kotu ta yi watsi da neman dakatar da takarar fidda-gwanin Obaseki a PDP

0

Babbar Kotun Tarayya ta Shiyyar Fatakwal ta yi watsi da dakatar da tsayawa takarar fidda-gwani da Gwamna Godwin Obaseki ya fito a karkashin jam’iyyar PDP da wani dan takara ya shigar a gabanta.

Kotu ta ce ba za Obaseki na nan daram a matsayin dan takara kuma da shi za a fafata a zaben Wanda zai cira tuta jam’iyyar PDP a zaben gwamna Mai zuwa.

Obaseki ya koma PDP ne bayan APC ta hana shi sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu a karkashin jam’iyyar.

Jam’iyyar PDP ta daga wa Obaseki kafa, inda ya shiga cikin ‘yan takara, kuma tuni har wani ya rigaya ya janye masa.

Sai dai kuma wani dan takara mai suna Omoregie Ihama, ya sha alwashin cewa ba zai yarda Obaseki ya fito takarar fidda gwani ba.

A kan haka ne ya garzaya kotu ya nemi a ta hana Obaseki tsayawa, saboda ya cewar sa, bai sayi fam ba, kuma lokacin da ya koma jam’iyyar PDP, an rigaya an rufe lokacin sayen fam na takara.

Sannan kuma Ihame ya ce sai wanda ya sayi fam zai iya tsayawa takara, sannan kuma ya shaida wa kotu cewa ya na tababar takardun makarantar Obaseki.

Sai dai kuma hakan da bai cimma ruwa ba, domin kotu ta yi watsi da wannan korafi da Kara da Ihama ya kawo gabanta.

A ranar Alhamis ne dai za a yi zaben fidda gwanin. Kuma kotun ta dakatar da Obaseki, har zuwa a ga hukuncin da za ta yanke a gobe Laraba, jajibirin zaben fidda-gwanin na PDP.

Can a cikin APC kuwa, tuni har sun tsayar da Mutum Ize-Iyamu dan takarar APC din a zaben gwamnan Edo da zai gudana a ranar 19 Ga Satumba, 2020.

Ize-Iyamu tsohon dan PDP ne, wanda Shugaban APC na Kasa Adams Oshiomhole ya daure wa gindin tsayawa takarar takara bayan ya raba hanya da Obaseki.

Share.

game da Author