SAMA DA FADI DA KAYAN ABINCIN TALLAFI: Kotu ta sa a kamo shugaban karamar hukuma a Kano

0

Kotun majistare dake jihar Kano ta bada umurnin a kamo shugaban karamar Hukumar Kumbotso Kabiru Ado-Panshekara, a dalilin sama da fadi da yayi da kayan abinci da za a raba wa talakawan karamar hukumar sannan da kin amsa gayyatar kotu.

Alkalin kotun Musa Ibrahim ya ce a taso masa keyar Ado-Panshekara saboda bijire wa kotu da yayi, yaki halartar gayyatar sa da tayi bayan an kawo karar sa na yin sama da fadi da yayi da kayan abin cin da ya kamata a raba wa talakawa.

Lauyan da ya shigar da karan Salisu Tahir ya bayyana cewa a ranar 9 ga watan Mayu an bai wa Ado-Panshekara fom guda 1,632 domin raba wa mutanen da ya kamata su samu tallafin Korona da gwamnati ke rabawa a karamar hukumar.

Tahir ya ce a shugaban karamar hukumar sai yayi gaban kansa ya ki yin abin da ya kamata ya waske da kayan abincin sannan ya raba wa wadanda ya ga dama abinda ya ga daman basu.

Lauyan dake kare Ado-Panshekara, Ibrahim Adamu ya ce bai san abinda ya hana Panshekara zuwa kotu ba.

Ya ce a safiyan Laraba ya kira daya daga cikin masu taimaka wa Ado-Panshekara a wayar sallula inda ya tabbatar masa da cewa suna hanyar zuwa kotun.

Hakan ya sa ya nemi alfarmar kotun ta dakatar da zaman ta na minti 30.

A dalilin rashin bayyanar Ado-Panshekara a kotun alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Mayu.

Share.

game da Author