Gwamnatin Saudiyya ta sanar da Najeriya cewa za ta maido ‘yan Najeriya sama da 11,000 zuwa kasar nan.
Sanarwar ta ce wadanda a dawo da su din sun kunshi wadanda suka yi saurin tafiya Umrah, amma suka makale a can, saboda babu halin dawowa.
Sun kasa barin Saudiyya ne saboda mahukuntar kasar sun kafa dokar hana jirage sauka da tashi a kasar.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ji cewa wadanda suka makale a kasar daga zuwa Umrah, ba su wuce su 340, sauran duk ‘yan Najeriya ne wadanda ke zaune kasar ba da cikakkun takardun iznin zaman kasar ba, wadanda aka ci sani da tikali
Tikari kan zame wa mahukuntan kasar karfen-kafa, idan suka shiga harkar dabanci da fadace-fadacen cikin unguwa, irin wanda ‘yan daba ke yi a biranen Arewacin kasar nan.
A Saudiyya ana kiran irin wadannan matasa ‘yan-agulla, kuma sun yi kaurin suna sosai. Mafi yawa a can aka haife su, kuma iyayen su duk ‘yan Arewacin Najeriya ne wadanda ke zaune a can ba da cikakken iznin zaman kasar ba.
Wani jami’i a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Saudi, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya sanar da wakilin mu cewa tabbas za a maido dandazon ‘yan Najeriya din gida ba da dadewa ba.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya tabbatar da cewa za a dawo da wadannan dandazon ‘yan Najeriya zuwa gida.
“Tabbas sun sanar da mu, amma sai mu ka roke su cewa ba mu yi wani shiri ko tanadin karbar su ba tukunna. Wannan shi ne ya haifar da jinkiri, amma ba don haka ba, da tun cikin makon da ya gabata za su fara sauke su a nan Najeriya.
“Ba mu kai ga yin tanadin karbar su ba, saboda na farko ba mu da wadatattun wuraren da za a killace dukkan su tsawon kwanaki 14, kafin a sallami kowa ya wuce gidan sa tukunna.
“Sannan kuma akwai matsalar karancin jami’an kuda da lafiyar da za su rika karakainar duba su, a lokacin da suke a killace.” Inji Ministan Harkokin Wajen Najeriya.
Ya kara da cewa Ofishin Jakadancin Saudiyya ya sanar da Najeriya batun dawo da wadanda suka je aikin Umrah su 340.
“To amma kuma hakikakin magana, wadanda za a maido din sun zarce mutum 11,000. Baya ga wadanda suka je Umrah, akwai kuma tulin ‘yan Najeriya da ke zaune a Saudiyya ba tare da cikakkun takardun iznin zaman kasar ba.
Tuni dai Saudiyya ta fara jigilar dimbin ‘yan kasashen Asiya masu aikace-aikace a kasar, ta na maida su kasashen su. Na baya-bayan nan da aka kwasa su ne ‘yan kasar Bangaladesh, wadanda ake kira Bangalai, kuma dama su da Indiyoyi, ‘yan Pakistan da kuma ‘yan Najeriya ne suka yi kaka-gida a kasar.
Sannan akwai kokarin da ake yi ba kwaso dabilan Najeriya wadanda ke karatu a can, da suka kammala karatun su, amma sun kasa dawowa gida saboda rufe filayen jiragen Saudiyya da na Najeriya.
PREMIUM TIMES ta gano yadda wasu daliban ke cikin halin kunci, inda tuni aka fitar da wasu daga dakunan kwanan su a jami’o’in da suke karatu.
Wasikar da Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya A Saudiyya, Reshen Jami’ar Imam Unibersity ya rubuta wa Ofishin Jakadancin Najeriya, ta nuna yadda daliban ke matukar son dawowa gida da kuma irin halin da su ke ciki.
Wasikar wadda Shugaban Kungiyar Dalibai Abdulhakim Adeokan ya dubuta, ta fado hannun PREMIUM TIMES.
Discussion about this post