Dan jarida Nasir Ibrahim dake aiki a gidan talbijin din Abubakar rimi dake Kano, ya kamu da cutar Coronavirus.
Ibrahim ya ce ya kamu da cutar ne bayan mu’amula da yayi da marigayi Rabiu Musa, tsohon hadimin marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua.
Ibrahim wanda wakilin PREMIUM TIMES ne a Kano ya shaida cewa gwajin da aka yi wa matar sa ma ya nuna ta kamu da cutar.
Ibrahim ya kai kan sa a yi masa gwajin jini bayan rasuwar Marigayi Rabiu Musa ganin ya yi mu’amula da shi marigayin kafin ya rasu.
Idan ba a manta ba Dan marigayi, Musa Rabiu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahaifinsa mai shekaru 60 a duniya ya fara jin zazzabi da makaki a makogoron sa. Bayan dan wani lokaci sai ya samu sauki. Haka kuma ba a dade ba sai ya ce yana jin numfashin shi na yankewa akai-akai, daga baya sai yace daukewa take yi kwata-kwata musamman idan ya gaji.
Marigayi Rabiu Musa ya rasu a asibiti a birnin Kano bayan fama da yayi da gajeruwar rashin lafiya.
Da misalin karfe 3 na dare Allah yayi masa cikawa a asibiti a Kano.
Musa ya ce ba a kai ga karbar sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa mahaifinsa ba ya rasu.