HARKALLAR P&ID: Kotun Amurka ta bai wa Najeriya iznin binciken asusun ajiyar su Jonathan da wasu kamfanoni

0

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin New York, ta amince Najeriya ta aika wa wasu bankunan Amurka sammacin neman sanin bayanan sirrin kudaden ajiyar wasu mutane da kamfanoni kimanin su 60.

Mai Shari’a na Kotun Tarayya ta Gundumar New York, Lorna Schofield ne ya amince da wannan roko da Najeriya ta yi.

Najeriya ta nemi sanin bayanan sirrin asusun ajiyar na su ne domin ta gani shin ko akwai hujjojin da za ta nuna wa kotu, domin a soke hukuncin biyan diyyar dala bilyan 9.6 da aka yanka wa Najeriya saboda karya yarjejniyar kwangilar kasa da kasa da Najeriya ta yi wa kamfanin P&ID.

Gwamnatin Buhari ta ki biyan diyyar, ta na mai cewa sama can kwangilar harkalla ce aka shirya tun 2010, wadanda suka shirya ta, sun san ba yiwuwa za ta yi ba.

A kan haka ne gwamnatin ke ta kokarin nuna wa kotu cewa kwagilar bogi ce wasu jami’an waccan gwamnati suka shirya tun cikin 2010.

Kotu na jiran Najeriya ta gabatar ma ta da hujjojin da za ta gamsu kafin ta soke diyyar dala bilyan 9.6 a kan Najeriya.

Dalla-dallar Yadda Harkallar Ta Dagule

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labari, makonni uku baya, yadda Gwamntin Najeriya ta aika wa bankunan Amurka wasikar bayanan sanin adadin kudaden da wasu kamfanoni da mutane 60 ta ke zargin sun boye daga salalar harkallar kwangilar P&ID, wadda a karshe ta zama alakakai.

Kin cika alkawarin yarjejeniyar yin kwangilar da Najeriya ta yi ne ya janyo wata kotu a Ingila ta yanke hukuncin za ta kwace kashi 30% bisa 100% na kudaden Najeriya da ke asusun kasar na kasashen Turai da Amurka.

Najeriya ta hakikice cewa kwangilar cike ta ke da harkalla a lokacin da aka kulla yarjejeniyar, lokacin tsohon Ministan Harkokin Man Fetur Rilwanu Lukman.

Najeriya ta ce dama can an kitsa kutunguilar kwangilar don a kasa aiwatar da ita, su kuma wadanda suka karbi salala, sun rigaya sun ci rabon su kenan.

A kan haka ne a yanzu Najeriya ta mike tsaye, fagamniyar neman hujjojin da za ta tabbatar wa kotu cewa dama can kwangilar ta bogi ce, kuma harkalla ce aka shirya.

Dalili kenan mahukuntan Najeriya suka tashi tsaye neman bayanan wasu da ake zargin sun karbi salalar la’ada-ciki da la’ada-waje, alhali a lokacin sun san kwangilar ba mai yiwuwa ba ce.

Cikin wadanda ake zargin sun ci kudin sun goge baki, har da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan da matar sa Dame Patience Faka Jonathan.

Hakan ya sa Najeriya ta rubuta wa wasu bankuna wasika a Amurka, kamar yadda PREMIUM TIMES HAUSA ta buga a ranar Alhamis.

Wuta ta kara ruruwa: A kokarin da Najeriya ke yi domin ganin kotu ta soke hukuncin biyan diyyar dala bilyan 9.6 ga kamfanin P&ID saboda rashin cika alkawarin yarjejeniyar kwangila, a yanzu haka PREMIUM TIMES ta mallaki kwafen wasikar da ta aika wa wasu bankunan Amurka 10, ta na neman bayanan kudaden da ta ke zargin wasu mutane da kamfanoni 60 sun kimshe a bankunan.

Samun wadannan bayanai idan har akwai su, zai iya gamsar da kotu cewa kwangilar ta bogi ce, don haka sai ta soke wancan hukuncin biyan diyyar makudan kudade kan Najeriya.

Kwafen wasikar ya nuna cewa wani fitaccen lauya mai suna Alexander Pence a karkashin Meister Seelig & Fein ne suka tsaya a matsayin lauyoyin Najeriya. Kuma ya aika da wasikar ga Babbar Kotun Amurka, wadda ya nemi ta amince ya aika wa bankunan kasar 10 tambayoyin abin sa ya ke so a ba shi game da bayanan kudaden mutanen da kamfanoni su 60.

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar Abubakar Malami na cikin lauyoyin Najeriya tare da gungun su Alexander Pence.

Wadanda ake neman sanin kudaden su a bankunan:

Akwai tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da matar sa Patience Jonathan. Sai tsohon Ministan Harkokin Fetur, Rilwanu Lukman, wanda shi ne ya sa hannun kwangilar a madadin Najeriya. Lukman dai ya rasu ‘yan shekarun baya.

Akwai Deizani Allison-Maduekwe, Ministar Fetur ta zamanin Jonathan, sai Taodiq Tijjani, Grace Taiga, Mohammed Kuxhazi da Micheal Quinn, wanda shi ma PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa ya mutu.

Sauran sun hada da James Nolan, Adam Quinn, Ibrahim Dikko da Ministan Shari’a lokacin Jonathan, Mohammed Adoke.

An dai shirya yarjejeniyar kwangilar lokacin da Shugaban Kasa na lokacin Umaru ‘Yar’Adua ke kwance ya na jiyya a kasar Saudiyya, cikin 2010.

An kuma ce har a kan gadon asibiti aka kai masa takardun gidogar kwangilar ya sa hannu alhalin bai san gidogar da aka kulla ba.
Rilwanu Lukman ne Ministan Fetur a lokacin ‘Yar’Adua.

Jaridar Bloomberg ta yi hira da kakakin kamfanin P&ID, wanda ya shaida mata cewa dama Najeriya ta daina neman ruwa a fako, ta biya kamfanin diyyar dala bilyan 9.6 da kotu ta yanka mata.

Jonathan da Patience dai sun musanta zargin sun boye kudade a wata kasa.

Ma’anar Wasikar Najeriya (Subpoena): Wata wasika ce mai kama da sammaci, amma ba samamci ba ce, tunda ba kotu ce ke aikawa da ita ba.

Ana aika ta ne a matsayin neman wasu bayanai ga wasi mutum ko wani kamfani domin a yi amfani da bayanan a warware wata kwatagwangwama a kotu.

Duk wanda aka aika wa wasikar ‘subpoena’, wajibin sa ne ya je kotun. Idan kuma bayanai ake so ya bayar to tilas ya bayar, matsawar dai tsakanin gidan sa da kotun ko ofishin sa da kotun ko kuma inda ya ke aiki da kotun bai wuce nisan mil 100 ba.

Share.

game da Author