Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Jibiya, Mustapha Jibia, ya tashi a zauren Majalisa ya ratattaki Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamna Aminu Masari da sauran Sanatoci da Mambobin Tarayya na jihar Katsina.
Da ya ke kokawa dangane da yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare a Jihar Katsina, musamman yankin garuruwan Jibia, Mustapha ya ce jami’an tsaron Najeriya ba su tabuka komai, har gara ma na Jamhuriyar Nijar su ke kai musu dauki idan ‘yan bindiga sun mamaye kauyukan su.
Ya ce abin haushi Gwamna Masari ya shigo gidan gwamnati, Buhari ya shige Abuja ba su tabuka wa Katsina komai.
Ya kuma koka a kan dukkanin wakilan.jihar da ke Abuja, da ba su fitowa su na fadar gaskiya.
Ya ce su ke da shugaban kasa, amma baya ga Barno, jihar Katsina inda Buhari ya fito ce aka fi kashe mutane.
Har gara Coronavirus ta kashe mu da mutuwa hannun ‘yan bindiga
Biyo bayan munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa garuruwan Katsina, Hakimin Batsari Tukur Mu’azu ya koka cewa jama’ar sa na kukan cewa har gara mutuwar Coronavirus da mutuwa a hannun ‘yan bindiga.
Mu’azu ya yi wannan kalami ne a cikin wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya, dangane da yadda mahara ke kai hare-haren kusan jama’a tare da kwace musu dabbobi da kuma zargin cin zarafin wasu.
Kananan Hukumomin Batsari, Jibia, Safana, Danmusa, Dutsinma duk su na fama da wadannan hare-hare na ‘yan bindiga.
“Jama’a ta sun gwammace Coronavirus ta kashe su, maimakon mutuwa a hannun ‘yan bindiga. Domin mu a Karamar Hukumar Batsari har yau Coronavirus ba ta kashe kowa ba. Amma ‘yan bindiga a kullum kashe mutane su ke yi, suna kwashe musu dukiya.
Ya yi kiran a kai agajin jami’an tsaro na sojojin, mobal da sojojin sama yadda za a yi wa maharan kwaf-daya.
Karamar Hukumar Batsari ta na cikin masifar hare-haren ‘yan bindiga. Garin Ruma ne na baya-bayan nan da aka kai wa farmaki.