CORONAVIRUS: Yadda Ba’Amurkiya ta mutu bayan ta kamu a dakin saurayin da ta kawo wa ziyara

0

Wata Ba’Amurkiya ta mutu a Warri, Jihar Delta, bayan ta kamu da cutar Coronavirus a dakin saurayin ta da ta yi tattakin kawo masa ziyata.

Ba’Amurkiyar wadda ‘gyatuma ce mai shekaru 60, ba a bayyana sunan ta ba, haka shi ma saurayin na ta wanda dan Najeriya ne, shi ma ba a bayyana sunan sa ba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Warri, Hafiz Inuwa, ya bayyana cewa saurayin ya saukar da Baturiyar a wani Otal a Warri, daga bisani kuma ya canja mata wani otal a wajen Warri, unguwar Ororekpe.

“Sun zauna a otal din tare tsawon mako guda, daga nan sai ta kamu da ciwon tari, sannan kuma ta rika samun wahalar yin numfashi da bayan-gida.

“An.garzaya da ita asibiti a ranar Asabar, amma da ya ke ta galabaita, ba da jimawa ba ta mutu.

Inuwa ya ce saurayin na ta ya na a hannun ‘yan sanda a Orerokpe. Sannan kuma ya ce ya sanar da Kwamishinan Lafiya na Jihar Delta, domin ya sanar da NCDC wasu alamomin ciwon da Baturiyar ta rika nunawa kafin mutuwar ta.

A karshe ya gargadi ‘yan sanda su yi kaffa-kaffa da saurayin wanda ke tsare, gudun kada su kusance shi har su kamu da cutar Coronavirus.

Ya zuwa ranar Lahadi, ranar da Baturiyar ta mutu, Coronavirus ta kashe mutum 143, ta kama mutum 4399, yayin da mutum 778 da suka kamu, sun wartsake.

Share.

game da Author