Tsohon gwamnan Barno, Mohammed Goni ya rasu

0

Gwamnan jihar Barno na farko, Mohammed Goni, ya rasu.

Marigayi Goni ya rasu bayan fama da yayi da rashin lafiya.

Ya rasu da misalin karfe 8 na daren Laraba a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Marigayi Goni ya zama gwamna a jihar Barno, a 1979, sai dai bai samu ya zarce ba a zaben 1983.

Marigayi Goni ya dawo fagen siyasa inda ya fafata da Kashin Shettima a 2011 na jam’iyyar APC.

Nan ma bai yi nasara ba duk da shine dan takaran gwamna na PDP a wancan lokaci.

Ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

Allah ya ji kan sa, Amin.

Share.

game da Author