CORONAVIRUS: Najeriya za ta yi wa mutum milyan 2 gwaji a cikin watanni 3 – NCDC

0

A kokarin da Najeriya ke yi wajen ganin ta dakile cutar Coronavirus, ta kudiri aniyar yin gwaji ga akalla mutum milyan 2 a cikin watanni uku.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana haka a lokacin da Kwamitin Shugaban Kasa mai Yaki da Coronavirus ke bayanin kowace rana da ke yi ga manema labarai ba.

“Masu gudanar da wannan aikin gwaji a dakunan gwajin cututtuka sun sha wannan alwashin na yi wa mutum milyan 2 gwaji a cikin watanni uku.

“Wannan kudiri kuwa da suka yi abu ne mai kyau da muhimmanci da karfafa guiwa matuka.” Inji Ihekweaze.

Sahihiyar kafar tattara bayanan alkaluman masu dauke da cutar Coronavirus a duniya, wato worldometre.org ta jaddada cewa Najeriya ce kasa mafi koma baya wajen karancin yi wa mutane gwaji, duk kuwa da cewa an samu masu cutar sama da 1,000 a cikin kasar.

Ranar Talata NCDC ta ce za ta yi wa mutum 3,000 gwaji a kowace rana, inda a Lagos kadai za a rika yi wa mutum 2,000 gwaji a kullum.

Sai dai kuma idan ba a manta ba, Najeriya ta bayyana cewa ta na fama da karancin kayan aiki, kamar yadda PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Najeriya na cikin matsancin fama da karancin kayan gwajin masu dauke da cutar Coronavirus.

Shugaban Hukumar Kula da Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihrkweazu ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja. Da ya ke karin bayani a shafin sa ba Twitter, Ihekweazu ya ce akwai matukar karancin kayan gwaji, wadanda ya ce ana bukatar karin masu yawan gaske domin a yawaita gwajin da ake yi a kowace rana a kasar nan baki daya.

Shugaban na NCDC ya kuma yi bayani dalla-dalla na irin kayayyakin gwajin da Najeriya ke bukata, sunayen su da kuma sunayen kamfanoni da masana’antun da ke yin su.

“Kayan gwajin da Najeriya ke bukata ruwa a jallo a halin yanzu su ne samfurin RNA wanda aka yi a kamfanin Qiagen ko na ThermoFischer, ko na SeeGene, ko na Inqaba ko na kamfanin LifeRiver da sauran su.”

Wannan bayani na Shugaban NCDC ya zo daidai lokacin da ake korafin cewa Najeriya ba ta tabuka abin kirki idan aka yi la’akari da yawan wadanda ta yi wa gwaji a kasar nan.

Kasashe da yawa wadanda ba su kai yawa da karfin Najeriya ba, irin su Ghana da Afrika ta Kudu, sum yi wa mutane da dama fiye da Najeriya gwaji.

Sama da mutum 1000 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya zuwa ranar Jama’a da ts gabata.

Najeriya ce koma bayan yawan wadanda aka yi wa gwaji a. Cikin kasashen da sama da mutum 1,000 suka kamu da Coronavirus.

Ranar 1 Ga Afrilu Najeriya ta ce za ta kara yawan mutanen da ts ke yi wa hwajo a kullum daga 500 zuwa 1,500.

Ranar Alhamis da ta gabata Najeriya ta ce za ts fara yi wa mutum 4,000 a kullum gwaji, inda a kullum za a yi wa mutum 2,000 gwaji a Lagos, sauran jihohi kuma mutum 2,000.

Sai dai kuma Kungiyar NIDS ta ce wannan magana duk tatsuniya ce, domin har zuwa yau mutanen da Najeriya ta yi wa gwaji kadan suka haura 10,000.

“In da a CE a kullum Najeriya na yi wa mutum 1,500 gwaji, kun ha ai a cikin sari uku za a iya yi wa mutum 30,000 gwaji kenan.” Cewar kungiyar.

Share.

game da Author