Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta rufe duk makarantun boko masu zaman kansu da na gwamnati dake kasar nan domin dakile yaduwar cutar Covid-19 a kasan.
Sai dai a cikin kwanakin nan ne wasu makarantu masu zaman kansu dake babban birnin tarayya Abuja suka fara kiran iyaye da su dawo da yara sannan su fara biyan su kudin makarantar zangon karshe na shekara.
Makarantun sun kuma aikawa iyaye da daliban su wasiku da su gaggauta biyan kudin makarantar yaran su da ga nan ne za fara koyar da yara darussan ta yanar gizo.
Mataimakin sakataren ma’aikatar ilimi na Abuja Umar Marafa ya bayyana haka ranar Talata.
Marafa ya ce gwamnati za ta dauki mumunar mataki akan duk makarantar da ta fara wani abu na koyar da dalibai ba tare da gwamnati ta ce ayi haka ba.
Ya ce barin makarantu irin haka su fara aiki zai kawo rudani a jadawalin karatu na yara a kasar nan.
A dalilin haka ma’aikatar ilimi dake Abuja ta yi kira ga makarantu masu zaman kansu su jira umarnin gwamnati tukunna.
Hukumar ilimi ta Abuja ta kammala shiri domin domin koyar da dalibai darussa ta hanyar yanar gizo, radiyo da talabijin a lokacin zaman gida.