COVID-19: Mutum 29 sun kamu, uku sun mutu a jihar Edo

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Edo Patrick Okundia, ya bayyana cewa mutum 29 ne ke dauke da cutar kuma 3 sun mutu a jihar.

Okundia ya fadi haka wa manema ranar Talata a garin Benin.

Ya ce tun da cutar ta bullo a jihar zuwa ranar 27 ga watan Afrilu an yi wa mutane 254 gwajin cutar inda sakamakon gwajin ya nuna 29 sun kamu.

“Daga cikin mutum 29 mutum 18 na kwance a asibiti kuma an sallami mutum 8.

” Mun kuma aika da jinin mutum 31 domin yi musu gwajin cutar.

Bayan haka matchmaking gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar Covid-19 dake jihar Philip Shaibu ya ce gwamnan jihar Godwin Obaseki zai tattauna da masu ruwa da tsaki da Kwararrun likitoci a jihar domin sassauta dokar hana walwala da gwamnati ta saka.

A ranar 19 ga watan Afrilu ne gwamnati ta saka dokar hana walwala a jihar domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Gwamnati ta saka dokar be Bayan kakakin medalists dokoki na jihar Frank Okiye ya kamu da cutar.

Okiye ya kamu da cutar ne bayan ya dawo da ka kasar UK.

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Litini

A bayanan da NCDC ta fita, Jihar Legas ta samu karin mutum 34, 2-Taraba, 2-Gombe, 11 – Barno, FCT – 15

Yanzu mutum 1337 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 255 sun warke, 40 sun mutu.

Share.

game da Author