Harbe dan shekara 10: Jama’an gari da ‘Yan sanda sun kacame a Jigawa

0

An barke da zanga-zanga a garin Sankara, karamar hukumar Ringim jihar Jigawa a dalilin zargin barbin wani yaro dan shekara 10 a kasuwa.

Mutane sun shaida cewa ‘yan sanda da suka zo kasuwar tarwatsa mutane a dalilin dokar da gwamnati ta saka na hana gwamatsuwa da juna da cin kasuwanni a fadin jihar ne daya daga cikin ha dirka wa yaron bindiga.

Mahaifin yaron ya ce an garzaya da yaron asibiti domin a duba a Ringim.

Sai dai kuma kakakin ‘yan sandan jihar, Audu Jinjiri, ya karyata wannan zargi yana mai cewa ki da yan sandan suka isa wannan kasuwa domin tarwatsa mutane, sai ka fara yi musu kuwwa, da jifar su da duwatsu.

Daganan ne fa suka jejjefa musu barkonun tsohuwa.

Ba harsashi bane ya samu wannan yaro, daya daga cikin duwatsun da suke jifar ‘yan sanda ne ya samu wannan yaro.

Share.

game da Author