Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana cewa daga yanzu duk wani matafiya da ya dawo jihar daga jihohin Kano da Legas sai an killace shi na tsawon kwanaki 14.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya shaida haka a taro da yayi da sarakuna da shugabannin addinai na jihar.
Ya ce hakan ya zama dole ganin yadda ake cin gaba da samun karuwar yaduwar annobar Coronavirus, sannan kuma hakkin gwamnati ne ta kare mutanen ta.
Ya umarci sarakunan su tabbata an killace duk wani matafiyi da ya ratso ta jihar daga Legas ko Kano.
Gwamna Sule ya ce ko da ko ‘yan uwan mu ne, muddun dai daga Legas ko Kano suka dawo a tabbata an dakatar dasu an kuma killace su na kwanaki 14.
” Yanzu haka mun dakatar da wasu matafiya 43 da suka dawo daga jihar Legas a garin Akwanga zasu wuce jihar Filato. Amma bamu yarda sun wuce ba. Mun Kira jami’ai daga jihar suka zo aka raka su har garin Jos inda aka killace su.
Ya ce akwai wasu kuma da bayan an tsare su sai suka arce cikin daji da gudun tsiya, suka arce. Kuma dukkan su daga Legas suke.
A karshe ya bayyana cewa ya yi irin wannan ganawa da shugabannin kananan hukumomin jihar domin samun hadin kai kan da hakan.