Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Litini.
A bayanan da NCDC ta fitar, Kano ta samu karin mutun 23, Kaduna 3, 5 a Gombe, Barno 2, Abuja 1, 1 a Sokoto, 1 a Ekiti.
Yanzu mutum 665 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 188 sun warke, 22 sun mutu.
Lagos-376
FCT-89
Kano-59
Osun-20
Oyo-16
Edo-15
Ogun-12
Kwara-9
Katsina-12
Bauchi-7
Kaduna-9
Akwa Ibom-9
Delta-4
Ekiti-4
Ondo-3
Enugu-2
Rivers-2
Niger-2
Benue-1
Anambra-1
Borno-3
Jigawa-2
Abia-2
Gombe-5
Sokoto-1
Jihar Kano dai tana ci gaba samun yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus. A sakamakon gwanjin ranar Litini, mutum 23 suka kamu da cutar.
Jihar Gombe, Sokoto da barno duk sun samu nasu rabon a ranar litini.
Jihar Kaduna ta samu karin mutum uku bayan ta sallami mutum hudu z makon da ya gabata. Gwamnan jihar Har yanzu bai sanar ko ya warke ko bai warke ba.
Idan baa manta a ranar Asabar ne aka yi jana’izar suhagaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Marigayi Abba Kyari.
Abba Kyari na daga cikin wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Ya rasu ranar Juma’a a Legas bayan fama da yayi da cutar na tsawon makonni biyu.
Wannan shine karon farko da za a bayyana wani ya kamu da cutar a jihar Barno.
Discussion about this post