Tun bayan saka dokar hana walwala da garkame jihohin Legas, Abuja da Ogun da gwamnati ta yi, shaguna da kantinan saida robobin saduwa da kai sun rancaba ciniki babu kakkautawa.
Kantuna irin haka sun yi cinikin da har karewa robobin suka yi ba maza ba ba mata ba.
Wakiliyar mu da ta zagaya wasu daga cikin wadannan shaguna kai tsaye da ta yanar gizo ta iske duk robobin sun kare tas-tas.
Masu shaguna sun bayyana cewa kasuwa fa ta bude musu matuka a dalilin barkewar coronavirus da kulle gari da aka yi.
” A makon da za a saka dokar hana walwala a jihohin Legas da Abuja. Mutane sun siya robobin saduwa da kai babu kakkautawa. An nemi robobin da ya kai ga har ma bani da su sun kare tas.” Inji Lami mai Kantin saida robobin saduwa.
” Yadda kasan mutane sun san za a garkame gari. Kowa ya rika garzayowa yana siyan robobin saduwa da kai, kala-kala. A rana daya sai da na siyar da rabin kayan shago na.
” Wannan Kasuwa da muka yi, na da nasaba yadda kowa zai garkame kansa a gida ne, saboda haka za a samu damar a rika shakatawa da robobin.
Su kansu matan aure da mazan su sun rika siyan wadannan robobi babu kakkautawa.
Wani mai kantin saida robobin saduwa a Abuja ya bayyana cewa wannan harka ta yi masa kyau, domin mazan aure sun koma ga matan su, an rabu da matan waje. Sannan kuma suma kan su da suke da mata sun siya sosai domin su ji dadin matan su.
” Wani abu da ya dan kawo mana cikas shine yadda muka samu karancin kaya. saboda nema da mutane ke yi abin ya kaiga ma babu ana matukan karancin shi a Najeriya. Abuja, Legas babu sauki.”
Ko a kasashen duniya, bincike ya nuna cewa kasashe kamar su Faransa, Jamus da sauransu duk sun rancaba ciniki matuka a dalilin zaman gida.