NNPC za ta damka matatun mai a hannun ‘yan kasuwa

0

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa, NNPC ya bayyana cewa za a damka matatun man kasar nan a hannun ‘yan kasuwa da zarar an kammala gyara su.

Mele Kyari ya ce NNPC za ta tsame hannun ta daga matatun, yadda yadda za a bukaci ‘yan kasuwa su shiga su zuba jari tare da kulawa, gudanar da shi da kuma dawainiyar kowace matatar.

Ya ce wannan baban rangwame ne aka samu sosai, kamar yadda Kyari ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na AIT.

Ya kara da cewa za a samu ‘yan kasuwar da za su tabbatar a bisa yarjejeniyar cewa za su kula da matarun ta yadda yadda za a dade ana cin moriyar su.

Sannan kuma su ne za su rika daukar dawainiyar gyara, kwaskwarima da kuma jidalin kula da su.

Idan ba a manta ba, dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi bakin jini a wajen ‘yan APC lokacin kamfen din zaben 2019, saboda ya ce idan ya ci zabe zai saida NNPC da matatun mai.

Gwamnati ta Daina Biyan Kudin Talafin Mai Har Abada

Shugaban Hukumar Kamfanin Mai na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa lokacin da gwamnati za ta biya kudin tallafin mai (oil subsidy), ya wuce, har abada ba za a kara biya a kasar nan ba.

Da ake tattaunawa da shi a gidan talbijin ranar Laraba, Kyari ya ce haka kawai an rika gabzar kudade ana bai wa wasu hamshakan ‘yan kasuwa da nufin talaka ya samu sassauci, amma bai samu sassaucin ba.

Kyari ya ce hamshakan dillalsn mai sun rika karbar kudsden talafin mai su na fantamawa abin su, tare da tara bargar jibga-jibgan motoci a gidajen su.

Ya ce idan gwamnati ta daina biyan kudin talalfin mai, zai ba ta dama bude wuraren hada-hadar cinikin fetur, Mega Stations a cikin kasashen da ke makautaka da Najeriya da yawa.

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta biya kudin talalfin mai har naida bilyan 720 cikin shekarar 2018.

Share.

game da Author