Mai horas da ‘yan wasan Westhampton United, David Moyes, ya kama aikin raba wa dattawa Mayan marmari da kayan miya a kauyen Lanchashire da ke Ingila.
Moyes, wanda tsohon mai horas da Everton da Manchester United ne, ya ce ya kama wannan aikin tuki ne domin ya taimaki tsofaffi a wannan lokaci na zaman gida dole da aka kakaba wa jama’a a Ingila.
Ya ce wata rana ya shiga wani kantin sayar da kayan marmari, sai ya ga ana neman direba.
“Sai na ji sha’awar na taimaka wa tsofaffi ta kama ni. Na je ba karbi aikin tukin.
“Abin ya na birge ni sosai. Zan tuka mota na yi lodin kayan marmari da kayan miya. Na rika bi kowane kofar gida na ajiye, na kwankwasa kofa, ko na danna kararrawa, na ce a fito a dauka.
“Akwai wata tsohuwar da ta taba dauko wani dan tukuici ta ba ni. Abin ya sosa min rai. Amma saboda ina so na dadada ma ta idan na karba, sai na sa hannu na amshe. Ni ina godiya, ita ma haka.
JOSE MOURINHO: Mai horas da Tottenham, kuma tsohon kociyan Chelsea, Manchester United, Inter Milan da Real Madrid, wato Jose Mourinho, zai fara tukin jigilar kayan abinci daga wani lambu da ke filin da kungiyar sa ke motsa jiki zuwa sitadiyan na Tottenham.
Ya bayyana haka a ranar Alhamis din nan, inda ya ce wannan wata gudummawa ce da zai rika bayarwa, ya na kwasar abinci zuwa sitadiyan, inda can ne sansanin tara kayan abinci da kuma dafawa ga marasa galihu.
Discussion about this post