Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga mutanen Bauchi da su kwantar da hankalin su a ci gaba da addu’oi Allah ya kawo karshen matsalolin da jihar ke fama da su.
Gwamna Bala ya kara da cewa ko a inda yake yana kan gaba wajen yakan matsalolin da jihar ke fama da su.
Kakakin gwamnan jihar Mukhtar Gidado,ya bayyana haka da ya ke sanar wa mutanen jihar sakon gwamna Bala.
” In Allah ya yarda zamu ga karshen wadannan fitintinu lafiya. Sannan ina rokon Allah madaukakin sarki ya sa wannan abu da ya same mu, ya zama kaffara a garemu.
Idan ba a manta ba gwamna Bala Mohammed ya kamu da cutar coronavirus bayan gwaji da aka yi masa.
Tuni dai aka killace ce a wuri daya inda ya ke samun kula.
Haka kuma akwai da dama cikin jami’an gwamnati da suka killace kansu domin tabbatar da rashin kamuwa da cutar.
Discussion about this post